An Gano Gawar Mutane 10 Bayan Harin Yan Bindiga a Kaduna

An Gano Gawar Mutane 10 Bayan Harin Yan Bindiga a Kaduna

  • Mutane sun shiga tashin hankali biyo bayan harin da wasu yan bindigan daji suka kai Unguwan Wakil, yankin Zangon Kataf a Kaduna
  • Gwamnatin karamar hukumar ta sanar da sanya dokar kulle tsawon awanni 34 nan take domin dawo da zaman lafiya
  • Bayanai sun nuna cewa lamarin ya samo asali ne daga wata rigima da ta haɗa ɗan sanda da ɗan Fulani

Kaduna - Aƙalla gawarwakin mutane 10 aka gano bayan wasu mahara da ake zaton Yan bindigan daji ne sun kai farmaki Unguwal Wakili da ke ƙaramar hukumar Zangon Kataf a Kaduna.

A wata sanarwa, gwamnati ta ce ta ƙaƙaba dokar zaman gida tsawon awanni 24 a garuruwan Ungwan Juju, Mabuhu, Ungwan Wakili da Zangon Urban kuma dokar zata fara aiki nan take.

Harin yan bindiga a Kaduna.
An Gano Gawar Mutane 10 Bayan Harin Yan Bindiga a Kaduna Hoto: punchng
Asali: Twitter

Mai taimaka wa shugaban karamar hukumar Zangon Kataf kan harkokin midiya, Yabo Chris Ephraim, ya ce an sanya dokar ne domin baiwa sojoji damar dawo da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Kotu ta Daure Jagororin Jam’iyyar PDP a Kurkuku a Dalilin Cin N140m Saboda Murde Zabe

"Wannan matakin zai ba dakarun rundunar sojin Najeriya damar dawo da zaman lafiya a yankin," inji Yabo Chris Ephraim, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa jami'in ɗan sanda ɗaya da fararen hula 10 ne suka rasa rayuwarsu ranar Asabar da daddare biyo bayan harin 'yan ta'adda a yankin.

Wannan harin na zuwa ne awanni 72 bayan wasu maharan sun halaka ɗan Fasto kuma suka yi awon gaba da wasu mazauna huɗu a kauyen Karimbu-Kahugu, ƙaramar hukumar Lere, Kaduna.

Wata majiya da ta nemi a ɓoye sunanta ta shaida wa jaridar Punch cewa lamarin ya fara ne da maraicen Asabar lokacin da saɓani ya shiga tsakanin jami'in tsaro da wani ɗan Fulani.

Majiyar ta ce saɓanin ya barke tsakaninsu a shingen bincike da ke Unguwan Wakil, wanda ta kai ga aka harbe ɗan sandan da kuma Bafullatanin a wurin.

Kara karanta wannan

Yanzun Nan: Tsageru Sun Kaiwa Ayarin Ɗan Takarar Gwamna Mummunan Hari a Kaduna, Sun Tafka Ɓarna

Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Bijilanti da Dama a Jihar Kaduna

A wani labarin kuma Yan Bindiga sun sake yin ajalin akalla yan banga 6 a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna.

Wani abokin aikin yan bangan, ya ce maharan sun bude musu wuta kan mai uwa da wabi, kuma baki ɗaya 'yan bangan da ke wurin sun mutu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel