Abu Namu: Gbajabiamila ya Kere Sa'a A Jerin Wadanda Zasu Iya Zamtowa Tinubu Shugaban Ma'aikata

Abu Namu: Gbajabiamila ya Kere Sa'a A Jerin Wadanda Zasu Iya Zamtowa Tinubu Shugaban Ma'aikata

  • Shugaban majalisar wakilai dai ya lashe zaɓen wakiltar yankin sa na Surulere 1 dake jihar Lagos ne a karo na 6
  • Biyo bayan nasarar tasa, sai yayi ɓatan dabo a wajen amsar shaidar lashe zaɓe da INEC ta raba ranar Talata
  • Ana ganin kujerar da yake nema yanzu itace ta shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa karkashin Tinubu

Alamu na nuni da cewa, shugaban majalisar wakilai na tarayya Femi Gbajabiamila ya shiga daga yan gaba-gaba na waɗanda zasu iya zamtowa shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa a mulkin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.

Ba'a ga fuskar Gbajabiamila ba sam a wajen amsar takardar shaidar cin zaɓe ba, a lokacin da INEC ta rabawa waɗanda suka ci zaɓen takarar da suka tsaya shaidar su domin dawowa majalisa ta 10 ba.

Kara karanta wannan

"Tunda mun ci zabe a baiwa Kirista shugabancin APC": Rikici ya kunno kai a uwar Jam'iyya

Gbajabiamila
Abu Namu: Gbajabiamila ya Kere Sa'a A Jerin Wadanda Zasu Iya Zamtowa Tinubu Shugaban Ma'aikata Hoto: Legit.ng
Asali: UGC

An dai sake zaɓar Gbajabiamila ne domin ya wakilci mazaɓar sa ta Surulere 1 dake jihar Lagos ne, a wani salo na ya wakilce su karo na 6 a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya samu kuri'u 19,717 ne dai, yayin da abokin karawar sa na kusa kusa Bosun Jeje na PDP, yasha kaye ƙuri'u 5,121.

Jaridar Leadership a ranar juma'a ta gano cewar, shugaban na majalisar ka iya watsi da majalisa, domin ana kyautata zaton zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sahale bashi muƙamin shugaban ma'aikatan Aso Villa a gwamnatin sa.

Wata majiya mai tushe daga gidan su Gbajabiamila ne ta tabbatar da zargin.

Gbajabiamila ya kasance ɗan amanar Tinubu na gaba-gaba, kuma tunda yayi aiki da duk wani dan siyasa a matakin tarayya shekaru 20 da suka wuce zuwa yau, hakan yasa Tinubu ke kallon sa a matsayin wanda yafi dacewa da muƙamin.

Kara karanta wannan

Shugaban Majalisa Ya Ki Karbar Satifiket Din INEC, Yana Harin Mukami Kusa da Tinubu

A cewar majiya:

"Muma abinda muke ji kenan. Idan kuka duba, baizo don amsar takardar lashe zaɓen da yayi ba ranar larabar data wuce. Kuma zancen gaskiya, baya buƙatar shaidar nan, domin yana da duk wata gogewa wajen zama shugaban ma'aikata ga zaɓaɓɓen shugaban ƙasa"
"...Bugu da ƙari, yayi aiki da duk wani dan siyasa a matakin tarayya shekaru 20 da suka gabata."

Lanre Lasisi, shine kakakin Femi Gbajabiamila, koda aka tambaye shi akan batun, yaƙi cewa komai.

"Kawai bai samu sukunin zuwa Abuja bane domin gudanar da taron," inji Lasisi.

An dai fara zaɓar Gbajabiamila zuwa majalisa ne a shekarar 2003. Tun daga wannan lokacin, yayi nasara a zaɓe guda biyar.

A tafiyar sa ta siyasa cikin shekaru 20, Gbajabiamila yayi bulaliyar majalisa, shugaban marasa rinjaye da kuma shugaban masu rinjaye na majalisar.

Sannan an zaɓe shi a matsayin shugaban majalisa a shekarar 2019.

Ramadan: Malamin Addini Yayi Kira Ga CBN a Saki Takardun Kuɗi Isassu

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito Fili, INEC Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Zaɓen Tambuwal Da Sauran Ƴan Majalisun Tarayya a Sokoto

Wani shahararren malamin addinin Muslunci nan mai suna Nurul Yaqeen dake jagorantar masallacin Jumma’a nan na Life Camp, Abuja yayi kira da kakkausar murya ga CBN dasu saki isassun kudi.

Malamin ya bukaci CBN daya taimaka ya saki isassun kuɗaɗe domin musulmi suyi siyayyar azumi da kuma ayyukan neman lada.

A cewar Nurul Yaqeen da ake wa laƙabi da Al-Yolawi:

"Inaso nayi amfani da wannan damar wajen kira ga gwamnatin tarayya da CBN wajen sakin isassun takardun kuɗi, domin watan Ramadan yana tunkaro mu gadan-gadan". Inji Nuru.

Asali: Legit.ng

Online view pixel