Dalilin Da Ya Sanya Muka Dakatar Da Zaɓen Ƴan Majalisun Tarayya Na Sokoto, INEC

Dalilin Da Ya Sanya Muka Dakatar Da Zaɓen Ƴan Majalisun Tarayya Na Sokoto, INEC

  • Hukumar INEC ta fito fili ta fayyace dalilin da ya sanya ta dakatar da zaɓen ƴan majalisun tarayya na jihar Sokoto
  • Hukumar tace ta lura da wasu abubuwa waɗanda akayi su ba bisa ƙa'ida ba a zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Hukumar ta kuma tabbatar da cewa ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zaɓen gwamna a jihar

Sokoto- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta ƙara fitowa fili ta bayyana dalilan da ya sanya bata sanar da waɗanda suka lashe zaɓe a zaɓen ƴan majalisun tarayya na jihar Sokoto. Rahoton Daily Trust

Gwamna Aminu Tambuwal yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi takarar sanata a jihar, amma an bayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammalu ba.

Shugaban INEC
Dalilin Da Ya Sanya Muka Dakatar Da Zaɓen Ƴan Majalisun Tarayya Na Sokoto, INEC Hoto: The Trent
Asali: UGC

A ranar Laraba, 8 ga watan Maris 2023, sabon kwamishinan INEC da aka tura jihar, Manjo Janar mai ritaya Modibbo Alkali, yayi bayani kan zaɓen na ranar 25 ga watan Fabrairu a wani taro na masu ruwa da tsaki.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: INEC Ta Samu Nasara, Kotun Ɗaukaka Kara Ta Yanke Hukunci Kan Buƙatar Peter Obi

Alkali yace an dakatar da zaɓukan ne bayan an gano wasu rashin gaskiya a cikin zaɓen.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yace shine dalilin da ya sanya aka cire kwamishinan hukumar zaɓen jihar da kuma sauran wasu abubuwa. Rahoton Vanguard

Yayi alƙawarin cewa hukumar zata inganta ayyukan ta domin gyara kura-kuran da aka lura da su domin tabbatar da cewa an gudanar da sahihin zaɓe a zaɓen gwamnoni dake tafe.

"Hukumar INEC ta ankara da ƙumbiya-ƙumbiyar akan lokaci sannan ta yanke shawarar dakatar da zaɓen ƴan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu." Inji shi
”Za ku ga cewa har yanzu babu wani ɗan majalisar tarayya daga jihar Sokoto da aka ba satifiket ɗin cin zaɓe."
”INEC tana yin duba kan zaɓen gabaɗayan sa da zummar shawo kan dukkanin matsalolin da aka samu domin tabbatar da sahihin zaɓe."

Kara karanta wannan

Abubuwa 6 Da Ya Wajaba Tinubu Tunkara Gadan-Gadan a Matsayin Shugaban Ƙasa

An dai samu rikici a zaɓen ranar 25 a jihar inda aƙalla rumfunan zaɓe 471 rikicin ya shafa.

2023: INEC Ta Soke Zabe a Mazabar Shugaban Masu Rinjaye, Ado Doguwa

A wani labarin na daban kuma, hukumar INEC ta soke zaɓe a mazaɓar, Alhassan Ado Doguwa, shugaban masu rinjaye na majalisar wakilan Najeriya.

Hukumar ta INEC tace sai an sake zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a mazaɓar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel