Mutane 61 Ne Suka Mutu Sakamakon Kamuwa da Cutar Mashako a Jihar Kano, Inji NCDC

Mutane 61 Ne Suka Mutu Sakamakon Kamuwa da Cutar Mashako a Jihar Kano, Inji NCDC

  • Yayin da ake ci gaba da jimami da ta’ajibin barkwar cutar mashako a Kano, hukuma ta fadi adadin wadanda suka mutu
  • Hukumar ta kuma bayyana kason jama’ar da suka kamu da wadanda suka warke daga asibitocin jihar Kano a Arewacin Najeriya
  • Ba wannan ne karon farko da annoba ke bullowa a jihar Kano ba, an sha samun wasu cututtuka daban-daban daga jihar

Jihar Kano - Akalla mutum 61 ne da suka mutu bayan da cutar ‘diphtheria’ wato mashako ta barke a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Salma Suwaid, jami’ar mai kula da annobar mashako a jihar Kano ce ta bayyana hakan a ranar Litinin yayin da tattaunawa da hukumar dakile yaduwar cututtuka masu harbuwa ta NCDC, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Kotu ba da belin dan majalisar Kano Doguwa, an ba shi sharadi kan zaben gwamnoni

Mashako wata annoba ce da ta bullo da ke shafar hanci, makogwaro da kuma fatar dan adam a wasu lokutan, kuma ta kan iya kisa idan bata samu daukin gaggawa ba.

Yadda cutar mashako ta kashe jama'a a Kano
Jihar Kano kenan da ke Arewa maso Yammacin Najeriya | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

Alamomin cutar mashako

Kadan daga alamominta sun hada da zazzabi, yoyon hanci, zafin makogwaro, tari, sauyawar launin idanu su koma ja, kumburin wuya da kuma wahalar numfashi.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Suwaid ta bayyana cewa, akalla mutum 783; maza 360 da mata 423 ne aka kwantar a asibiti a jihar ta Kano dalilin cutar, rahoton Punch.

Ta kara da cewa, akalla wadanda suka kamu da cutar sukan shafe kwanaki hudu ne a asibiti kafin a sallame su ko kuma rai ya yi halinsa bayan shafe kwanakin da suka haura hudu.

A cewarta, kaso 83% na wadanda suka mutu sun kamu da cutar ne sama da kwanaki uku, kuma suka shafe kwanaki fiye da 15 a asibiti.

Kara karanta wannan

An Kuma: 'Yan Bindiga Sun Sake Kai Sabon Mummunan Hari a Jihar Kaduna

Hakazalika, ta ce an yi nasarar sallamar kaso 68% na wadanda suka kamu, yayin da kaso 1.66% suka tsere sai kuma kaso 12.2% da suka rasa rayukansu.

Matakin da ake dauka

Adejoke Oladele, mai wakiltar hukumar lafiya ta bai daya ta NPHCDA ta ce, hukumar na aiki tare da NCDC wajen rage yaduwar annobar mashako tare da yada rigakafinta a jihar.

An shiga jimami da tashin hankali lokacin da aka gano barkwar cutar ta mashako a jihar Kano, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

Baya ga annobar mashako, annobar yawaitar kode fatar jiki ta yi yawa a Kano, an shawarci masu ‘bleaching’ da su rage saboda hakan zai jawo mummunar asara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel