Ku Yi Hattara da Macewar Sassan Jiki da Ciwon Daji, NAFDAC Ta Gargadi Masu ‘Bleaching’

Ku Yi Hattara da Macewar Sassan Jiki da Ciwon Daji, NAFDAC Ta Gargadi Masu ‘Bleaching’

  • Hukumar NAFDAC ta gargadi mutanen da ke amfani da mai ko wani nau'in kayan sauya fata da su kula
  • Hukumar ta ce mutane na iya fuskantar kalubalen lalacewar fata ko jawo wa kai ciwon daji daga amfani da kayan 'bleaching'
  • Wasu bakaken Afrika na daukar bakar fata a matsayin muni, suna amfani da kayan kwaile fata don kara kyau

Jihar Legas - Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) ta gargadi 'yan Najeriya game da amfani da kayan kwalliya da sinadarai masu hadari wajen kwaile fata don kara kyau.

Wannan na fitowa ne a jiya Lahadi 25 ga watan Satumba daga bakin babban daraktan hukumar, Farfesa Majisola Adeyeye a wani taron kwana biyu da hukumar ta shirya a Legas.

NAFDAC ta gargadi masu 'bleaching'
Ku yi hattara da macewar gabobi da ciwon daji, NAFDAC ta gargadi masu bilicin | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta yi gargadin cewa, sinadaran da ke tattare layan kwaile fata na dauke da ababen da ke sa cutar daji a fatar dan-adam, ya lalata gabobi har ma ya kai ga mutuwa, inji rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Buhari ya fusata, ya ce shugabannin jami'o'i su bude makarantu a koma karatu

A cewarta:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Ba mu haramta kayayyakin don kawai suna kwaile fata ba ne, mun haramta su ne saboda tsaro ganin irin sinadaran hadin da ke cikin kayayyakin na iya kawo cutar daji har ma da ciwon hanta da koda."

Yadda ake samun kayan kwaile fata

Ta kuma bayyana cewa, galibi ana shigo da kayan kwaile fata ne ta barauniyar hanya ba tare da sanin NAFDAC ba.

Ta kuma kara da cewa, irin kayayyakin yanzu sun zama annoba tsakanin maza da mata a Najeriya, wanda kuma abin damuwa ne.

A bangare guda, ta zargi masu harkar kwalliya da gyaran jiki da amfani da kayayyakin kwaile fata, inda suke gwamutsa su da karas, gwanda da sauran 'ya'yan itatutuwan gyaran fata.

A cewarta, ana wankar jama'a ne kawai ana siyar musu kayan kwaile fata da sunan man gyaran fata daga kayan itatuwa, musamman a shafukan intanet.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya Sun Gaji da Abubuwan da ke Faruwa a Kasar nan, Atiku

Ta ce wannan lamari na masu kayan gyaran fata ya wuce gona da iri, har ya kai ga suna iya hada kai da ma'aikatan kiwon lafiya wajen tallata hajarsu.

Hakazalika, ta ce hukumar na fuskantar kalubale saboda irin wadannan masu sana'ar gyaran fata suna yiwa daidaikun mutane ne a boye, don haka zai ba hukumar wahala ta gano inda ake ajiye kayan a shaguna.

Wasu bakaken fata a Afrika, musamman Najeriya na yawan neman mayukan gyaran fata da zai sauya su daga bakake zuwa farare.

Gwamnatun Najeriya Ta Ce Cin Fatan Dabbobi Bai da Wani Amfani, Za a Haramtawa ’Yan Najeriya

A wani labarin, gwamnatin Najeriya na shirin kawo kudirin dokar da zai haramta cin fatar dabbobi da aka fi sani Ponmo a kasar saboda habaka masana'antun fata.

Muhammad Yakubu, babban daraktan cibiyar fata da kimiyya ta NILEST dake Zaria ne ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Satumba, TheCable ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Budurwa ta shiga damuwa, ta hada kayataccen biki amma kawayenta suka ki hallara

Ya kuma bayyana cewa, cibiyar da yake kula da ita da kuma sauran masana'antun fata za su tunkari majalisar dokokin kasar da na jihohi don tabbatar da haramcin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel