Alkalin Kotun Daukaka Kara Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu a Akure

Alkalin Kotun Daukaka Kara Ya Yanke Jiki Ya Fadi, Ya Mutu a Akure

  • Alkalin Kotun daukaka kara mai zama a Akure, babban birnin jihar Ondo, Ayobode Lokulo-Sodipe, ya mutu
  • Bayanai sun nuna cewa Marigayin ya yanke jiki ya faɗi yayin da yake shirin shiga zaman Kotu a Ofishinsa ranar Litinin
  • Kungiyar lauyoyi reshen Akure ta tabbatar da faruwar lamarin kuma ta yi ta'aziyya ga iyalansa

Ondo - Alkalin Kotun ɗaukaka kara da ke jihar Ondo, Mai shari'a Ayobode Lokulo-Sodipe, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar The Cable ta tattaro cewa a ranar 15 ga watan Fabrairu, 2023 marigayi Lokulo-Sodepe, ya cika shekara 67 a duniya.

Ayobode Lokulo-Sodipe.
Alkalin Kotun daukaka kara mai zama a Akure, Ayobode Lokulo-Sodipe Hoto: Thecable
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa Alkalin ya yanke jiki ya faɗi a Ofishinsa yayin da yake shiri tare da sanya kayan Alkalai domin shiga zaman Kotu ranar Litinin.

Duk yunkuri na aka yi na ceto rayuwarsa bayan ya faɗi bai kai ga nasara ba kuma Allah ya masa rasuwa tun kafin waɗanda suka ɗauke shi su kai Asibiti.

Kara karanta wannan

2023: INEC Ta Ɗage Lokacin Zabe a Jihohin Najeriya 16? Gaskiya Ta Bayyana

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon shugaban ƙungiyar lauyoyi (NBA) mai reshe a Akure, babban birnin jihar Ondo, Rotimi Olorunfemi, ya tabbatar da faruwar lamarin a wani saƙo da ya fitar.

Ya ce:

"Yanzun nan na tabbatar da batun (rasuwar Alƙali), da gaske ne Allah ya masa rasuwa. Ya yanke jiki ya faɗi a Ofishinsa da ke Kotun ɗaukaka kara a Akure."
"An yi kokarin garzayawa da shi Asibiti amma daga isa Likitoci suka tabbatar da rai ya yi halinsa."

Haka nan shugaban NBA reshen Akure na yanzu, Banji Ayenakin, ya tabbatar da mutuwar Alkalin a wata sanarwa.

"Labarin mutuwar mai shari'a Lokulo-Sodepe ya zo mun da kaɗuwa, shugabana mutumin kirki ne mai basira da sanin ya kamata. Ina ta'aziya ga iyalansa da shugaban kotun ɗaukaka ƙara."
"Baki ɗaya iyalan kungiyar NBA zasu yi kewar kokari da jajircewar marigayin wajen ci gaban bangaren shari'a a Najeriya."

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

A watan Fabrairu, 2008, aka naɗa Lokulo-Sodipe a matsayin Alkalin Kotun daukaka ƙara, kamar yadda Thisday ta ruwaito.

Mai juna biyu ta rasu a layin zabe

A wani labarin kuma Wata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Kan Layin Zabe a Zamfara

Wata matar aure mai ɗauki da juna biyu, Shamsiyya Ibrahim, ta rasu yayin da take kan layi tana jiran kaɗa kuri'a a garin Tsafe, jihar Zamfara.

Wani mazaunin garin ya shaida mana cewa ana tsaka da zaɓe matar ta faɗi, mutane suka yi kokarin kai ta Asibiti amma rai ya yi halinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel