Ba Gaskiya Bane: INEC Ba Ta Tsawaita Lokacin Zabe a Jihohi 16 Ba

Ba Gaskiya Bane: INEC Ba Ta Tsawaita Lokacin Zabe a Jihohi 16 Ba

  • INEC ta karyata labarin da ake yaɗawa a soshiyal midiya cewa ta tsawaita lokacin zabe a jihohi 16
  • Mai magana da yawun INEC, Rotimi Oyekanmi, ya ce labarin kanzon kurege ne kuma ya kamata mutane su yi fatali da shi
  • A jiya Asabar ne hukumar zabe ta ƙasa ta gudanar da zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya

Abuja - Hukumae zabe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ce ba ta ɗaga lokacin zabe a jihohin Najeriya 16 ba kamar yadda wasu ke yaɗawa, a cewar rahoton The Cable.

Wata sanarwa da ta yi ikirarin cewa INEC ta tsawaita lokacin kaɗa kuri'a a zaben shugaban kasa da yan majalisun tarayya na ƙara yaɗuwa a manhajar Whatsapp.

Rumfar zabe.
Malaman zabe suna aiki a rumfar zabe. Hoto: thecable
Asali: UGC

A cewar sanarwan, INEC ta amince da ƙara lokacin zaɓen zuwa Lahadi 26 ga watan Fabrairu, 2023 duba da faɗace-faɗacen da aka samu a wasu rumfuna da rashin zuwan malaman zabe a kan lokaci.

Kara karanta wannan

Mutuwa Rigar Kowa: Wata Mata Mai Juna Biyu Ta Yanke Jiki, Ta Rasu a Layin Zabe a Zamfara

Wane jihohi lamarin ya shafa

Bugu da ƙari sanarwan ta bayyana jihohin da matakin tsawaita lokacin ya shafa, sun haɗa da, Legas (Surulere, Ikate, Okota, Eti-Osa, Kosofe da Oshodi), Abuja, Ebonyi, Ribas, Imo, Anambra, Kano da kuma Edo.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sauran jihohin su ne, Delta, Kogi, Bayelsa, Enugu, Sakkwato, Taraba, Abiya, da kuma jihar Ekiti.

"Zabe a wadannan wuraren da abun ya taba zai ci gaba da karfe 8:00 na safe zuwa 12:00 na tsakar ranar 26 ga watan Fabrairu, 2023," inji sanarwan.

Menene gaskiyar wanɓan sanarwa da aka jingina wa INEC?

Amma lokacin da jaridar ta tuntubi Festus Okoye, kwamishinan INEC na kasa kuma shugaban sashin yaɗa labarai da wayar da kan masu kaɗa kuri'a ya ce labarin ƙanzon kurege ne.

Haka zalika mai magana da yawun INEC na kasa, Rotimi Oyekanmi, a shafinsa na Tuwita ya bukaci yan Najeriya su yi watsi da labarin.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Faɗa Ya Kaure Tsakanin Magoya Bayan NNPP da APC a Jihar Kano

Ya ce:

"INEC ba ta tsawaita lokacin zaɓe a jihohi 16 ba, wannan labarin da kuke gani ƙarya ne bai da tushe. Inda ake iya kara lokacin zabe shi ne wurin da ba'a buɗe rumfa da karfe 8:30 na safe ba."
"Duk mai kaɗa kuri'an da yake a kan layi kafin karfe 2:30 na rana dole zai jefa kuri'arsa ko karfe nawa ne kuma ko da ya wuce lokacin rufewa."

A wani labarin kuma Bola Tinubu Ya Lashe Zaben Kananan Hukumomi 10 a Jihar Ekiti

Baturen zaben jihar ya bayyana cewa Tinubu ne ya samu kuri'a mafi rinjaye, Atiku ya take masa baya a matsayim na biyu, kana Peter Obi na uku da Kwankwaso da ya zo na huɗu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel