Kotu Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Zama Gidan Gyaran Hali Bisa Zagin Mahaifinsa

Kotu Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Zama Gidan Gyaran Hali Bisa Zagin Mahaifinsa

  • Wata kotun majistare ta yankewa wani matashi hukuncin zama a gidan gyaran hali kan wata aika-aika da ya tafka
  • Matashin ya dubi tsaɓar idon mahaifin sa sannan ya ɗura masa zagi ta uwa ta uba bayan sun samu saɓani
  • Majistare ya yanke masa hukunci domin zuwa gidan gyaran hali ya saito tarbiyyar sa wacce ta gurɓata

Plateau- Wata kotun majistare a jihar Filato ta tura wani matashi mai shekara 35 zuwa gidan gyaran hali bisa ɗurawa mahaifin sa zagi.

Matashin mai suna Fwangmun Danung, an kuma tuhume sa da yiwa mahaifin sa barazana. Rahoton Daily Trust

Majistare Tapmwa Gotep, ya yankewa Danung hukuncin shekara ɗaya a gidan gyaran hali bayan ya amsa laifin da ake tuhumar sa da shi.

Kotun Majistare
Kotu Ta Yankewa Wani Matashi Hukuncin Zama Gidan Gyaran Hali Bisa Zagin Mahaifinsa Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Majistaren ya yanke masa hukuncin wata shida a gidan gyaran hali da zaɓin biyan tarar naira dubu goma bisa zagin mahaifin sa, sannan da hukuncin wata shida a gidan gyaran ba tare da zaɓin biyan tara bisa yiwa mahaifin sa barazana.

Kara karanta wannan

Rikicin PDP: Kwana 2 Gabanin Zabe, Gwamna Wike Ya Sake Ta da Wa Atiku Hankali

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tunda farko, mai shigar da ƙara, Insp Frank Alex, ya gayawa kotun cewa s ranar 26 ga watan Disamban 2022, told the court that on December 26, 2022, wanda ake ƙarar ya fitar da mahaifin sa da ƙarfin tsiya daga gidan sannan ya zazzage shi.

Matashin ya kuma yi barazanar ƙona gidan idan mahaifin nasa bai bashi naira dubu ɗari biyu ba (N200,000).

Laifin a cewar mai shigar da ƙarar ya saɓawa sashi na 377 da 379 na dokar Penal Kod ta jihar Plateau.

Alƙalin kotun ya bayyana cewa hukuncin zai zama matsayin gargaɗi ga masu son aikata irin wannan rashin tarbiyyar a nan gaba. Rahoton The Punch

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

A wani labarin na daban kuma, gwamnatin tarayya ta bayyana irin hukuncin da ta tanadar wa gwamnonin da suka riƙa sakin baki yayin nuna adawa da sauya fasalin takardun kuɗin naira.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gidan, Sun Harbe Shugaban Jam'iyya Har Lahira

Gwamnatin tarayyar ta bayyana hakan ne ta hannun babban lauyanta kuma ninistan shari'a na ƙasa, Abubakar Malami (SAN).

Gwamnonin jihar Kaduna da Kano sune ke a kan gaba wajen saki baki yayin nuna adawa da shirin na sauya fasalin takardun kuɗin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel