DSS Ta Cafke Na Hannun Daman Kasurgumin Shugaban Yan Bindigan Zamfara Kachalla

DSS Ta Cafke Na Hannun Daman Kasurgumin Shugaban Yan Bindigan Zamfara Kachalla

  • Hukumar DSS ta sanar da cewa ta kama wasu masu yi wa yan bindigan Zamfara safara makamai
  • Wanda aka kama din shine wani Aliyu Yahaya da ake ce na hannun daman kasurgumin shugaban yan bindiga, Kachalla Damina ne
  • Kakakin DSS, Peter Afunanya ya lissafa bindigu da harsashi da gurneti da wasu makamai da aka samu tare da wanda ake zargin

Zamfara - Hukumar tsaron farin kaya, DSS, ta ce ta kama wani Aliyu Yahaya mai safarar bindigu kuma na hannun daman Kachalla Damina, kasurgumin dan bindiga da ake zargi yana adabar mutanen Dansadau da kewaye a Zamfara.

Mai magana da yawun hukumar ta DSS, Peter Afunanya ne ya sanar da hakan yayin wata jawabi da ya yi a ranar Alhamis, The Cable ta rahoto.

Jami'an DSS
Jami'an DSS sun kama wanda ake zargi da sayarwa yan bindiga makamai. Hoto: The Punch.
Asali: UGC

Afunanya ya ce kayayakin da ako kwato hannun Yahaya sun hada da:

Kara karanta wannan

Kano: DSS Ta Gano Bindigu, Takubba Da Sauran Muggan Makamai A Ofishin Kamfen

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Bindiga kirar GPMG guda daya, charbi na harsashi, harsashi na GMPG guda 190, harsashi na AK 47 guda 28 da gurneti guda daya."

Ya kuma cigaba da cewa a Kaduna, an kama yan aiken yan bindiga - Tukur Usman da Iliyasu Adamu a karamar hukumar Chikun a ranar 20 ga watan Fabrairu, ya kara da cewa an samu harsashi guda 372 masu tsawon 7.62 X 39mm da harsahi na GPMG guda 26 a hannunsu.

Ya ce wadanda ake zargin suna daga cikin masu sayarwa yan bindigan jihar Zamfara makamai, kuma an fara kama su ne a ranar 22 ga watan Janairu a hanyar Barkin Ladi - Pankshin, a jihar Plateau suna hanyar kai wa kwastomominsu makaman.

Afunanya ya ce an kwace harsashi 612 na GPMG 120 da AK-49 da suka boye a cikin buhun shinkafa a hannunsu a lokacin.

Kara karanta wannan

Zaɓukan 2023: Kimanin N500bn ne Aka Tanada DOn Sayen Kuri'u, Shugaban EFCC Bawa

DSS ta kama bindigu, wukake, takubba da wasu muggan makamai a ofishin kamfen a Kano

A wani rahoton kun ji cewa hukumar yan sandan farin kayan, DSS, ta yi nasarar gano wasu muggan makamai da aka boye a wani gida da ake amfani da shi matsayin ofishin kamfe a Kano.

The Punch ta rahoto cewa mai magana da yawun hukumar DSS Peter Afunanya ya ce hukumar ta samu bayanan sirri ne kafin ta kai samame gidan da ke hanyar Airport Road, karamar hukumar Nasarawa a Kano.

Asali: Legit.ng

Online view pixel