Atiku Ya Fada Mana Ayyuka 8 Da Ya Yiwa Arewa Lokacin Yana Mulki: Kashim Shettima

Atiku Ya Fada Mana Ayyuka 8 Da Ya Yiwa Arewa Lokacin Yana Mulki: Kashim Shettima

  • Kashim Shettima ya kalubalanci dan takarar shugaban kasan jam'iyyar PDP ya fito fili ya amsa wasu tambayoyi
  • Shettima ya ce yan Arewa su daina cewa zasu zabi Alhaji Atiku Abubakar saboda dan Arewa ne
  • A cewar tsohon gwamnan na Borno, babu abinda Atiku ya tsinanawa Arewa lokacin da yake mulki

Sokoto - Dan takaran kujerar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress APC, Kashim Shettima, ya caccaki dan takarar shugaban kasan PDP, Atiku Abubakar.

Shettima ya ce masu cewa zasu zabi Atiku kawai don dan Arewa ne basu san wanene dan takaran PDPn ba.

Ya kalubalanci Atiku ya fadawa yan Najeriya ayyukan takwas da ya yiwa Arewa lokacin da ya rike kujerar mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru takwas.

Shettima ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a filin kamfen APC a jihar Sokoto ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

A cewarsa:

"Atiku ya yi shekara 8 a matsayin mataimakin shugaban kasa, ya kirga ayyuka takwas da ya yiwa Arewa. Ya kirga mutum 8 da ya gina a Arewa."

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Naka, naka ne amma ba nakan da ya san aljihunsa kadai ba."
Atinuu
Atiku Ya Fada Mana Ayyuka 8 Da Ya Yiwa Arewa Lokacin Yana Mulki: Kashim Shettima Hoto: @APCPresCC22
Asali: Twitter

Lokacin sakawa Tinubu Alherin da yayi ya iso

Kashim Shettima ya bayyana cewa idan al'ummar Arewa bata zabi Tinubu ba basu kyauta ba.

Ya ce zai zama butulci saboda Tinubu ya goyi bayan yan Arewacin Najeriya tun zamanin Yar'adua, Nuhu Ribadu, Atiku da kuma Buhari a 2015.

Shettima ya lissafo yadda Tinubu ya sanya al'ummar yankin kudu ta yamma suka ka'dawa Buhari kuri'a a zaben 2015.

A cewarsa:
"A 2015, Kasar Yarabawa da Edo da Tinubu ke jagoranta suka bamu kuri'u miliyan 2 da muka kayar da Jonathan da su.

Kara karanta wannan

Takarar Shugaban Kasa: Mai Goyon Bayan Atiku, Reno Omokri Ya Soki Peter Obi, Ya Yaba Wa Bola Tinubu

"Lokacin sakamako ya yi, mu hada karfi da akrfe, mu cire kanmu daga kunya, a sanmu da kunya da dattaku."
"Jama'a a takaice, Allah ya ce a Suratul-Rahman: Sakamakon Alheri, Alheri ne."
"Mu nuna cewa yan Arewa masu amana ne, Tinubu ya yi mana hallaci."

Abinda zamu yiwa yan Najeriya

Shettima ya ce idan suka smau nasara a zaben 2023, zasu inganta rayuwan mutanen Najeriya.

"Idan Allah ya bamu mulki, zamu rike amana, zamu kula da al'umma."
"Zamu samawa dubban matasa abun yi, za'a tallafawa yan kasuwa, zamu share hawayen malaman boko da islamiyya."

..Yace.

Asali: Legit.ng

Online view pixel