Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

Abin da ya sa Tinubu Ya Jawo Hadimansa Suna Cin Mutuncin Shugaban kasa - Atiku

  • Atiku Abubakar ya ce Bola Tinubu ya taimaka wajen cin mutuncin shugaban kasa da wasu ke yi
  • ‘Dan takaran PDP a zabukan 2019 da 2023 ya ce Tinubu ya fusata ne saboda an hana shi magudi
  • Wazirin Adamawa yana ganin bankin CBN ya kawowa APC cikas wajen amfani da kudi a zabe

Abuja - Atiku Abubakar mai neman shugabancin Najeriya a jam’iyyar APC, ya zargi Asiwaju Bola Tinubu da jawowa Muhammadu Buhari batanci.

Rahoto ya zo daga Daily Trust cewa ‘dan takaran jam’iyyar adawar ya ce Asiwaju Bola Tinubu ya ba mukarrabansa kwarin gwiwar sukar shugaban kasa.

Alhaji Atiku Abubakar ya ce ba komai ya sa ‘dan takaran kujerar shugaban kasar yake wannan ba sai saboda CBN ya fito da tsarin da zai yi maganinsa.

Phrank Shaibu ya fitar da jawabi a madadin kwamitin takarar Atiku Abubakar, yana cewa Bola Tinubu yana so ne ya yi amfani da kudi a zabe mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ina son gaje kujerar Buhari: Tinubu ya nemi goyon bayan sarkin Musulmi, sarkin ya ba shi amsa

CBN sun yi maganin APC?

A daidai lokacin nan ne kuma Gwamnan babban bankin Najeriya ya fito da tsarin da ya takaita yawon kudi, Shaibu ya ce wannan ya fusata Bola Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimi Atiku Abubakar ya ce ba komai ya jawo Bayo Onanuga yana sukar Godwin Emefiele da Abubakar Malami ba sai saboda an toshe masu hanya.

Tinubu
Tinubu da Buhari a Sokoto Hoto: @officialasiwajubat
Asali: UGC

Mai taimakawa ‘dan takaran na PDP wajen yada labarai yake cewa da farko mutanen Tinubu sun fara ne da cin mutuncin Gwamnan CBN, Godwin Emefiele.

An koma kan Osinbajo da Buhari

Daga baya sai ya ce an shiga bata Yemi Osinbajo saboda bai bin su wajen yawon kamfe. Rahoton nan ya zo a jaridar Punch a yammacin Alhamis.

"Bayan nan kuma sai su ka je gidan talabijin su na zargin Sakataren shugaba Buhari, Tunde Sabiu da juya akalar gwamnati, wannan abin dariya.

Kara karanta wannan

Gaskiya Ta Fito: Shugaba Buhari Ya Faɗa Wa Sarkin Musulmi Abu 3 da Suka Sa Ya Shiga Kamfen Tinubu

Festus Keyamo shi ne karamin Ministan kwadago. Har mai gidansa, Chris Ngige ya nesanta kan shi daga tallar Tinubu, ya ce bai da ‘dan takara.
Amma Keyamo ya cigaba da aiki a matsayin Kakakin kamfe duk da cewa irinsu Tinubu da Bayo Onanuga su na ta caccakar shugaba Buhari."

- Phrank Shaibu

Shaibu ya ce idan za a soki Malami, ta ya suke zama da shi a taron FEC, kuma idan aka kushe gwamnatin Buhari, tamkar an kushe Ministan tarayyar ne.

Shari'ar hana amfani da tsohon kudi

A karshen makon nan aka samu rahoto Muyiwa Adekeye ya fitar da jawabi ya ce mutanen Jihar Kaduna sun yi maraba da hukuncin kotun koli.

Nasir El-Rufai ya ce tsarin canjin manyan kudi ba zai amfanar da tattalin azikin kasa ko kuma talakawa ba, don haka suka kai karar bankin CBN a kotu.

Kara karanta wannan

Buhari a Sokoto: Tinubu ya Matukar Fahimtar Matsalolin Najeriya, Ku Zabe Shi

Asali: Legit.ng

Online view pixel