Buhari ya Bukaci ‘Yan Najeriya sun Dinga Godewa Allah, Ya Fadi Halin da Wasu Kasashe Ke Ciki

Buhari ya Bukaci ‘Yan Najeriya sun Dinga Godewa Allah, Ya Fadi Halin da Wasu Kasashe Ke Ciki

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci ‘yan Najeriya da su dinga godewa Allah duk da halin da suka tsinci kansu a ciki
  • Buhari ya sanar da cewa, a kasashen da ke da makwabtaka da Najeriya fama suke da cin abinci sau daya a rana amma ba hakan bane a Najeriya
  • Ya sanar da cewa, a shawagin da yayi a jirgin sama a Kano, ya ga manyan gine-gine da ke nuna cigaba ba kadan ba a fannin kayan more rayuwa

Kano - Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Litinin yayi kira ga ‘yan Najeriya da su gode kan halin da suke ciki a kasar nan idan suka duba yadda wasu kasashe suke.

Shugaba Buhari
Buhari ya Bukaci ‘Yan Najeriya sun Dinga Godewa Allah, Ya Fadi Halin da Wasu Kasashe Ke Ciki. Hoto daga Channelstv.com
Asali: UGC

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a dakin taron Banquet na Kano bayan kammala ziyarar da ya kai ta kaddamar da ayyuka a jihar.

Kara karanta wannan

Babu Gwamnati da Zata Iya Shawo kan Dukkan Kalubalen Najeriya ita Daya, Shugaba Buhari

Kamar yadda Femi Adesina, hadimin shugaban kasan ya sanar a wata takarda, Buhari ya kwatanta cigaba a ababen more rayuwa a fadin kasar nan matsayin abun alheri.

“Muna da gagarumar kasa amma ba mu godewa har sai Mun ziyarci kasashen da muke makwabtaka da su inda jama’a ke cin abinci sau daya a rana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A yayin da nake helikwafta, yawan manyan gine-ginen da na gani da yawan cigaba da na hango a kasa abun farin ciki ne. Mun godewa Allah, Mun godewa Allah, Mun godewa Allah.”

- Shugaban kasan yace.

Channels TV ta rahoto cewa, Buhari yayi kira ga masu kudi da su karfafawa matasa guiwa inda yace ko Mun so, ko mun ki sai sun bar musu kasar.

“Dole ne su rungumi ilimi saboda amfanin ilimi. Fasaha ta kawo sauki amma babu abinda zai mana ye gurbin koyo. Don Allah ku karfafa guiwar yaranmu su yi karatu.”

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama ainihin mutanen da ke boye sabbin kudi, suna siyarwa a boye a Arewa

- Yace.

Ya taya Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano murna kan ayyukan da yayi a bangaren more rayuwa inda ya kara da cewa ziyarar da ya kai baya-bayan nan a Kogi, Yobe, Legas da Katsina sun nuna cewa gwamnonin sun yi kokari da iyakar iyawarsu.

Ganduje ya ziyarci Buhari, Yace Kanwa sun shirya tarbarsa

A wani labari na daban, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano ya Kaiwa Buhari ziyara har gidansa da ke Daura a jihar Katsina.

Ya sanar masa cewa an shirya tsaf don karbar bakuncinsa a babbar Cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel