Kotu Ta Daure Dagaci Kan Kin Biyan Bashin Wanda Ya Ranta Masa Kudi Ya 'Siya' Sarauta A Adamawa

Kotu Ta Daure Dagaci Kan Kin Biyan Bashin Wanda Ya Ranta Masa Kudi Ya 'Siya' Sarauta A Adamawa

  • Kotu ta yanke wa dagajin kauye hukuncin daurin shekaru takwas a gidan gyaran hali a jihar Adamawa
  • Sunaka, wanda ya shigar da kara a kotun ya ce Gumni Ilihu ya karbi tumakinsa 13 ya siyar don ya samu sarauta
  • Amma bayan Ilihu ya samu sarautan sai ya ki biyan Sunaka kudinsa har ma ya yi barazanar zai kore shi daga garin

Adamawa - Kotun majistare a jihar Adamawa yanke wa wani dagajin kauye, Gumni Ilihu, na kauyen Gugu, yankin Banjiram a karamar hukumar Guyuk daurin shekara takwas a gidan yari saboda cin amana, makirci da firgitarwa.

Wani malamin firamari mai suna Roel Sunaka, dan shekara 47, ya kai Ilihu kara a kotu kan rashin biyansa tumaki 13 da ya sayarwa dagajin, rahoton The Punch.

Gudumar Kotu
Bayan Cin Bashin Kudi Don Siyan 'Sarauta', Dagaci Ya Yi Barazanar Korar Wanda Ya Bashi Rance Daga Garin. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

Kamfen zub da jini: An sheke wani, da dama sun jikkata a kamfen PDP a wata jihar APC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sunaka, wanda supervisor ne a makarantar firamare ta Bobini a karamar hukumar Guyuk, ya ce bayan ilihu ya yi amfani da kudin da ya sayar da tumakin ya samu sarauta, ya ki biyansa kuma ya fara masa barazana cewa zai kore shi daga garin.

Yayin da ya ke yanke hukunci, Hyellamada Hyellandendu ya samu wanda aka yi karar da laifin cin amana.

Hyellandendu ya ce:

"Saboda cin amana, kai Cif Gumni Ilihu, an yanke maka daurin shekaru biyar da zabin biyan tara ta N100,000, daurin shekara guda saboda barazana da zabin tarar N25,000, sai daurin shekaru biyu na makirci da zabin biyan tara na N50,000."

Alkalin kotun ya ce wanda aka yanke wa hukuncin zai yi zaman gidan yarin a gwamutse.

Ya yi barazanar kora ta daga kauyen mu idan na ciagaba da tambayarsa kudi na, Sunaka

Kara karanta wannan

Abba Kyari Ya Yi Mani Alkawarin N10m Domin Yi Wa Bukola Saraki Sharri – ‘Dan Fashi

Da ya ke magana da yan jarida kan shari'a, Sunaka ya ce:

"Na tafi kotu saboda shi Gumni (Ilihu) ya sayar da tumaki na 13 a 2013 ya yi amfani da kudin ya nemi sarauta a matsayin dagaci wato Sarki Gugu. Na yi kokarin nema ya biya ni amma ya ki.
"Sau da yawa, bayan ya zama dagaci, ya yi barazanar sai kore ni daga kauyen idan na cigaba damunsa ya biya ni kudin da na bashi."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164