CBN Ya Ce Akwai Sabbin Kudi a Kasa, Bankuna Sun Ki Zuwa Dauka, Suna Ba da Tsoffi
- Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ce yana da tarin sabbin Naira a dankare a maa’ajiyarsa a hakin da ake ciki a kasar
- Babban bankin ya ce ya sha kiran bankunan kasuwanci a kasar nan da su zo su karbi sabbin kudin tare da ba ‘yan Najeriya da ke bukata
- A cewar bankin na CBN, duk bankin da aka kama yana ba da tsoffin kudade a ATM zai fuskanci hukunci mai tsanani da aka tanada
Duk da cewa wa’adin da CBN ya dauka na daina amfani da tsoffin na matsowa, bankunan kasar nan ba sa zuwa karbar sabbin kudin da aka buga, a cewar babban bankin.
Daily Trust ta ruwaito cew, CBN ya ce ya sha rokon bankunan kasar nan da su zo su dauki sabbin kudaden amma ba sa zuwa.
A shekarar 2022, CBN ya sanar da yin sabbin kudaden Naira da suka hada N200, N500 da N1,000, sun fara aiki a ranar 15 ga watan Disamba, tsoffi kuma za su yi sallama da amfani a ranar 31 ga watan Janairun bana.
Yayin da har yanzu ake ci gaba da kai ruwa rana game karbar sabbin kudin, karancin kudin ma na daga cikin abin da mutane suka fi mai da hankali a kai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
CBN na sanya ido kan bankunan kasuwanci a Najeriya
Da yake magana a wani taron wayar da kan jama’a game sa sabbin kudi a Legas, shugaban tawagar doka ta CBN a jihar, Kofo Salam-Alada ya ce babban bankin zai tsanantawa bankunan kasuwanci da ke koron sabbin kudin a ATM.
Ya bayyana cewa, babban bankin ya shirya daukar matakin kakaba tara da hukunci kan bankunan da ke kin ba kwastomomi sabbin kudi a ATM, rahoton Vanguard.
A cewar Salam-Alada:
“Zan iya fada muku a yau cewa a kullum CBN na ba da sabbin kudi. Da nake magana daku, bankuna na can a CBN don karbar kudin.
“Muna ma rokon bakuna ne da su zo su dauki kudin daga Babban Bankin. Muna da sabbin kudin nan a ma’ajiyarmu kuma muna rokon bankuna da su zo su dauke su.
“Mun gano akwai abubuwa da yawa da ke faruwa da suke bukatar mu magance, don haka muka hana cire sabbin kudi a kan kantadon tabbatar da kowa zai samu kudin ba wai wani mai kudi da ya san manaja ba, da zai shigo ya debe dukkan sabbin kudin a bankin reshe.
“Wannan ne yasa muka ce kudaden su zauna a ATM wanda ta hakan ba zai bambanta mutane ba.”
Salam-Alada ya kuma bayyana cewa, babban bankin na ci gaba da sanya ido kan batunan domin gano yadda sabbi da tsoffin kudade ke yawo a kasar.
Tuni wani dan kasuwa a jihar Gimbe yace shi zai daina karbar kudin daga ranar 25 ga watan Janairun 2023.
Asali: Legit.ng