A Ina Aka Fadi Haka? Yan Najeriya Sun Caccaki Malamin Addini Kan Hana Ma'aurata Kwanciyar Aure

A Ina Aka Fadi Haka? Yan Najeriya Sun Caccaki Malamin Addini Kan Hana Ma'aurata Kwanciyar Aure

  • Yan Najeriya da dama suna fushi da Fasto David Ibiyeomie na cocin Salvation Ministries
  • Ku tuna cewa a kwanan nan ne Ibiyeomie ya hana ma’aurata yin tarayya da junansu na tsawon kwanaki 21 yayin da cocin ya fara azumi
  • Da suke martani, yan Najeriya sun ce wannan umurni baya cikin littafi mai tsarki kuma ko da zai yi aiki a kan marasa aure ne

Ba sabon labari bane cewa babban faston cocin Salvation Ministries da ke Port Harcourt, Fasto David Ibiyeomie, ya hana ma’aurata kwanciyar aure na tsawon kwanaki 21 yayin da cocin ya shiga azumi da addu’a.

Da suke martani ga hakan, yan Najeriya da dama sun yi ikirarin cewa dalilansa basa da hurumi a cikin littafi mai tsarki. A cewarsu, kamata ya yi ace wannan doka zai yi aiki ne a kan marasa aure.

Kara karanta wannan

Atiku, Tinubu, Obi: CAN Ta Magantu Kan Yan Takarar Shugaban Kasa, Ta Fada ma Matasa Wa Za Su Zaba

Fasto David Ibiyeomie
A Ina Aka Fadi Haka? Yan Najeriya Sun Caccaki Malamin Addini Kan Hana Ma'aurata Kwanciyar Aure Hoto: David Ibiyeomie
Asali: Facebook

Ku tuna cewa Ibiyeomie ya ce:

“Ku kauracewa mu’amalar aure a wannan lokaci na azumi saboda na ji mutane na cewa ‘mijina ya ce da zaran mun sha ruwa tunda mun ci abinci, mu ci wannan ma’! Don haka, na ji wannan! A matsayina na Fasto, sun ce mani dan Allah ka yiwa mijina magana cewa muna azumi!

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Kwanaki 21 ba zai kashe ku ba!’ Ku guji zuwa wannan bangaren! Rayuwa ba a kansa bane. Yanzu ba lokaci ne na kwanciya da mazaje da matayenku ba! Kun ji abun da nake fadi? Daga gobe ku rufe wannan wajen har sai bayan kwana ashirin da daya!”

Ga martanin wasu yan Najeriya

Adaora Clara Sommie Anyim:

“Amma Allah ne ya yi umurnin ayi aure. Kamata ya yi ace wannan umurni ya yi aiki a kan marasa aure. Ina ganin ya kamata mutane su daina zakewa a kan wasu abubuwa. Irin wanna umurnin zai kawo matsaloli a wasu auren. Wanda ake magana a kai miji/matarka ce, ba daduro ba. Allah ya halasta kwaciyar aure ga ma'aurata kawai.

Kara karanta wannan

Bayan Sun Shafe Shekaru 10 da Aure Harda Yara 2, Ma'aurata Sun Gano Cewa Iyayensu Daya

Juliet Onyekachi:

"Abuj da Allah ya hada, kada a bari mutum ya kawo tangarda da irin wannan yanayi...Ba zai hana ku yin addu'o'inku ba..kawai ku yi amfani da wannan kwanaki 21 ku chanja munanan dabi'unku, ku taimakawa mabukata sannan ku yada soyayya a tsakani. Wannan shine abun da Allah yake kallo ba abun da kuke yi da abokan zamanku ba."

Ngobua Nora Nabem:

"Ban gane ba wato idan mutum na azumi laifi ne ya kwanta da matarsa ta sunna ko miji?"

PJ More:

"Ba ka da kowani yanci na hana ma'aurata sauke hakokinsu na aure."

A wani labari na daban, wasu ma'aurata da suka kwashe tsawon shekaru 13 tare harda yara biyu sun gano akwai alaka ta jini a tsakaninsu.

Kamar yadda suka bayyana a wani bidiyo da ya yadu a soshiyal midiya, sun gano cewa su din yaya da kanwa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel