Zaben 2023: Ku Guji Siyar Da Kuri’unku - Kungiyar CAN Ga Matasa

Zaben 2023: Ku Guji Siyar Da Kuri’unku - Kungiyar CAN Ga Matasa

  • Shugabancin kungiyar kiristocin Najeriya ya sake aika gagarumin saki ga Kiristoci a kasar
  • A wani sako, Kungiyar CAN ta bukaci matasan Najeriya da kada su siyar da kuri’unsu a zabe mai zuwa
  • Kungiyar ta kuma ba yan Najeriya tabbacin cewa sadaukarwar da suka yi ba zai tafi a banza ba, cewa kuri’unsu zai yi amfani

Abuja - Kungiyar Kiristocin Najeriya(CAN) ta yi kira ga matasa a kan kada su yarda su siyar da kuri’unsu a babban zabe mai zuwa.

Babban sakataren matasan CAN reshen Abuja, Joseph Daramola, ne ya yi kiran a yayin wani gagarumin gangamin matasa a Abuja a ranar Lahadi, 8 ga watan Janairu.

Yan takarar shugaban kasa
Zaben 2023: Ku Guji Siyar Da Kuri’unku - Kungiyar CAN Ga Matasa Hoto: Rabiu Kwankwaso, Mr. Peter Obi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Atiku Abubakar
Asali: Facebook

CAN ya baiwa matasa aiki gabannin zaben shugaban kasa na 2023

Ya bayyana cewa an gasawa matasan Najeriya aya a hannu don haka, sun matsu su yi abun da ya dace a yayin da ake tsaka da fargabar rashin sanin me gobe za ta haifar, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Hawaye Sun Kwaranya Yayin da Yan Bindiga Suka Halaka Amarya da Ango Yan Kwanaki Kafin Aurensu

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

CAN ta ce:

“Wannan ne dalilin da yasa muke karfafawa matasa gwiwa. Idan wani ya so baku cin hanci, ku ce a’a! Idan wani ya nemi ku siyar da kuri’unku, ku ce a’a!
“Ku na da yancin tabbatar da ganin Kun yi abun da ya kamata ku yi sannan ku zamo masu karfin gwiwa a kan haka.”

CAN ta fada ma matasa wanda za su zaba a 2023

Damarola ya bayyana cewa kowace jam’iyyar siyasa na da yancin zabar duk wanda suke so a matsayin abokin takara, addini guda ko akasin haka, rahoton The Guardian.

Ya Kara da cewar:

“Abu guda a matsayin kiristoci kuma shugabannin matasa shine cewa ya zama dole mu umurci mutanenmu da su fita sannan su zabi son ransu.”

Legit.ng ta tattauna da wasu matasa don jin yadda suka dauki wannan shawara ta CAN inda suka ce lallai akwai hikima a zancen.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Ce Ya Cika Alkawuran da Ya Dauka, Tinubu Ya Ce ba Haka Abin Yake ba

Mallam Salis ya ce:

"Maganar CAN gaskiya ce, ya kamata matasa su waye, su gane cewa, wanda ya siya kuri'arka ba zai maka aiki ba sai ya mayar da kudinsa.
"Ya kamata mu zama shugabanni masu tasiri a cikin al'ummarmu. Duk kudin dan siyasa da ikonsa, matukar muka kama kanmu, muka zama masu tunani ba za su iya juya mu ba.
"Amma a irin wannan yanayin, babu wulakantacce irin matashi, aiki ma ya gagari matashi balle kuma maganar ya iya zama shugaba, gashi ana cewa matasa kashin bayan al'umma, amma an mai da abin ya zama matasa jidalin al'umma. Allah yasa mu gane, mu ji maganar CAN da duk sauran masu kira ga matasa su zama masu kamun kai."

Ku zo mu hada hannu don ci gaban jam'iyyarmu, PDP ta roki gwamnonin G5

A wani labarin, mun ji cewa yayin da babban zaben kasar ke kara gabatowa, jam'iyyar PDP ta fara kokarin sulhu da shugabanni da gwamnoninta da suka fusata.

Babbar jam'iyyar adawa a kasar ta roki gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike da sauran gwamnonin G-5 a kan su zo su hada hannu don cimma manufarsu na son ceto Najeriya a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel