Matakai 5 da Za a bi Wurin Siyan Kadarorin da EFCC ta Kwace Daga Mahandama

Matakai 5 da Za a bi Wurin Siyan Kadarorin da EFCC ta Kwace Daga Mahandama

  • EFCC ta ce a shirye take da fara siyar da wasu daga cikin kadarorin da suka kai matakin karshe na umarnin kwacewa
  • A halin yanzu, hukumar yaki da rashawar ta bukaci 'yan Najeriya da suka shirya siyan kadarorin da su ziyarci shafinta na yanar gizo tare da sauke fom din siya
  • Hukumar ta bayyana cewa za ta rufe saida fom din kadarorin da aka kwace a ranar 8 ga watan Janairun wannan shekarar

Hukumar yaki da rashawa tare hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), ta sanar da shirinta na fara siyar da kadarorin da suka kai matakin kwacewa.

Legit.ng ta gano yadda hukumar yaki da rashawar ta bayar da dama ga wadanda ke da ra'ayin ko kungiyoyi da su shigar da bukatarsu don siyan kadarorin da aka kwace.

Kara karanta wannan

2023: Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki, Ta Tona Asirin Mai Hana Ruwa Gudu a Rigingimun PDP

Abdulrasheed Bawa
Matakai 3 da Za a bi Wurin Siyan Kadarorin da EFCC ta Kwace Daga Mahandama. Hoto daga Economic and Financial Crime Commission
Asali: Facebook

Kamar yadda hukumar ta bayyana, za a rufe shigar da bukatar tayin kadarorin a ranar Litinin, 9 Janairu, 2023.

Jern kadarorin

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

A cewar EFCC, kadarorin sune jerin gidaje kayatattu guda 16, jerin gidaje da filaye a fadin kasar.

  • Jerin kayatattun gidaje 24 a Banana Island dake Legas.
  • Kayatattun gidaje guda 21 a manne da juna da sashin gidaje a Thornburn, Yaba dake Legas.
  • Jerin gidaje 16 masu dakuna hudu manne da juna a rukunnan gidajen Heritage Court a Port Harcourt, dake jihar Ribas.

Saura sun hada da gidaje da filaye a Legas, cikin alkaryar Abuja, Anambra, Ebonyi, Gombe, Kaduna, Delta da jihar Edo.

Haka zalika, akwai otel, shaguna da gidaje a Kwara, gidaje da filaye a Osun, Oyo da fadin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Rudani: Majinyata sun rude, gobara ta kama a babban asibitin kwararrun jihar Arewa

Waye zai iya siyan kadarorin?

Jama'ar al'umma zasu iya shigar da bukatarsu don tayin sai dai idan EFCC ta taba gurfanar da kai ko kungiyar ko kuma ana shari'a tsakaninka da hukumar EFCC; irinsu kamfanonin da shugabannin ma'aikatan kamfanonin hukumar yaki da rashawar.

Yadda za a iya shigar da bukatar siyan kadarorin da EFCC ta kwace

Matakin shigar da bukatar tayin kadarorin akwai gasa mai yawa a ciki, hakan yasa masu shigar da bukatarsu ya kamata su bi wadannan matakan:

  1. A ziyarci shafin yanar gizo na EFCC don sauke fom din tayin da tabbatar da rantsuwa ga mai siya ko wani kamfani karkashin kamfanonin da aka jero. Je ka Gwanjon EFCC gami da aje fom da kashi 10 na kudin tayin da sanannun asusun banki wanda za a biya ga EFCC.
  2. Idan kudin ya haura N10 miliyan, akwai bukatar samar da wasu takardun bankin. Masu tayin da ba suy i nasara ba za a mayar musu kudin su bayan gama tayin kadaririn.
  3. Wadanda suka yi nasara kuma zasu cika sauran kashi 90 na kudin tayin cikin kwanaki 15 na kwanakin aiki kafin ranar rufewa, rashin yin hakan na nufin ba za a maido da kashi 10 da suka bada na kudin tayin ba, sannan za a ba wani mai shirin siya damar mallakar kadarar.
  4. Mutanen dake zaune a jerin kadarorin da aka lissafo suna da damar kin tashi idan har suna da yarjejeniyar zama; su biya hayar shekarar sannan su cije bukatar mallakar kadarar a manhajar EFCC.
  5. Dole ne a kammala cinikin kadara tare da mika ta ga adireshin hukumar: Hukumar Yaki da Rashawa Tare da Hana yi wa Tattalin Arzikin kasa Ta'annati, dake Plot 301/302 Institutions and Research District, Jabi, Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel