Fadan Su Wike Ba Da Atiku Bane, Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki a Rigimar PDP

Fadan Su Wike Ba Da Atiku Bane, Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki a Rigimar PDP

  • Tsohuwar Minista kuma jigo a jam'iyyar PDP ta tabo batun rikicin cikin gida da ya hana babbar jam'iyyar adawa zaman lafiya
  • Olajumoke Akinjide, ta ce tawagar G5 da ta kunshi gwamnoni 5 ba su da matsala da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa
  • Ana ci gaba da dakon jin wanda tsagin gwamna Wike zasu mara wa baya bayan zaman sulhu ya ruguje

Ibadan, Oyo -Tsohuwar karamar ministar Birnin tarayya Abuja, Olajumoke Akinjide, ta yi bayanin cewa rigimar fusatattun gwamnonin jam'iyar PDP biyar da ake wa lakabi da G5 bai shafi Atiku Abubakar ba.

Jaridar Vanguard ta rahoto Tsohuwar ministar na cewa duk wannan kace-kace da fushin tawagar G-5 suna yinsa ne kan shugabancin PDP na kasa karkashin jagorancin Dakta Iyorchia Ayu.

G5 da Ayu.
Fadan Su Wike Ba Da Atiku Bane, Tsohuwar Minista Ta Tsoma Baki a Rigimar PDP Hoto: PDP
Asali: Facebook

Babban abinda ke hana ruwa a gudu a yunkurin neman maslaha a PDP shi ne kujerar shugaban jam'iya, wanda G5 suka tsaya kai da fata dole sai an sauya.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Khadijat, Matashiyar Da Ta Nemi Takarar Shugaban Kasa Ta Samu Babban Mukami a PCC

Ta ya za'a kawo karshen wannan matsala?

Olajumoke ta ba da tabbacin cewa cikin ruwan sanyi zasu shawo kan rigingimun da suka dabaibaye babbar jam'iyyar adawa a matakin ƙasa kafin zaben shugaban kasa a ranar 25 ga watan Fabrairu.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Olajumoke Akinjide ta yi wannan furucin ne a wurin taron manema labarai da ya gudana a Ofishin kungiyar 'yan jarida dake Ibadan, babban birnin jihar Oyo jiya Talata.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa an kira taron yan jarida ne domin karin haske kan tattalin yanci na Atiku/Okowa wanda aka gudanar a Birnin Ibadan.

A kalamanta, tsohuwar Ministar ta ce:

"Mutanen da ya kamaya a ga suna ta rigima tun daga sama har kasa su ne jam'iyar APC. Batun da ya hana jam'iyar PDP zaman lafiya bai taka kara ya karya ba kuma abu ne da ya dace a kawo karshensa a cikin gida."

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: 'Yan Bindiga Sun Yi Wa Shugaban Jam'iyyar PDP Yankan Rago a Jihar Arewa

"Rigingimun PDP duk sun ta'allaka ne kan Ayu, amma ba ruwan dan takarar mu na shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar."
"Ko lokacin da Atiku, tsohon mataimakin shugaban kasa ya zo nan Ibadan, ya fada da bakinsa cewa ba bu wata matsala tsakaninsa da gwamnomin G-5."

An Fallasa Sunan Dan Takarar Shugaban Kasan Da Tinubu Zai Amfani Da Shi Ya Lashe Zaben 2023

A wani labarin kuma Ministan Buhari ya ce Obi ne babban makamin da APC zata yi amfani da shi Tinubu ya zama shugaban kasa

Karamin ministan ƙwadugo kuma kakakin kamfen Tinubu/Shettima, yace duk wani mai hankali da nazari ya san an riga an gama zaben 2023.

Festus Keyamo yace Obi ya zama babban makamin da APC zata amfana da shi Tinubu ya lashe zaben domin ya raba kan magoya bayan Atiku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel