Matashi Ya Kwanta a Bakin ‘Gate’, Ya Garkame Kofar Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shigowa

Matashi Ya Kwanta a Bakin ‘Gate’, Ya Garkame Kofar Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shigowa

  • Wani matashi ya haddasa yar dirama yayin da mai neman auren kanwarsa da yan uwansa suka zo ganinta a gida
  • Ya rufe ainahin babban kofar shiga gidan sannan ya kwanta a gabansa yayin da suke rokonsa kan ya barsu su shiga cikin gidan
  • Duk roko da kokarin da mutane daban-daban suka yi masa ya ci tura har zai da suka aikata masa wani abu mai ban mamaki

Wani matashi ya haddasa cece-kuce yayin da manemin kanwarsa ya zo gidansu tare da mukarrabansa.

A wani bidiyo da ya yadu a TikTok, matashin ya hana su shiga gidan yayin da ya shimfida tabarmarsa sannan ya yi bacci abun sa a gaban ainahin mashigin gidan.

Matashi
Matashi Ya Kwanta a Bakin ‘Gate’, Ya Garkame Kofar Don Hana Maneman Auren Kanwarsa Shigowa Hoto: TikTok/@livingwith_keneilwe
Asali: UGC

Wani mutum da ake ganin shine mai shirin zama angon kanwar tasa da wasu maza cikin shigar kwat da wando sun roke shi a kan ya barsu su shiga amma sam abun ya ci tura.

Kara karanta wannan

Miji Ya Manta Da Matarsa A Hanya Bayan Ta Sauka Kama Ruwa

Ya juya masu baya yayin da ya ki saukowa daga kan tudun na ki da ya hau. Bayan dan wani lokaci, daya daga cikin mazan da ke sanye da kwat ya jefa wa matashin damin kudi ta saman kofar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya tashi sannan ya yi shirin tafiya amma sai ya koma inda ya kishingida. Sai byan da aka sake jefo masa kudi a karo na biyu ne sannan ya barsu suka shiga.

Legit.ng ta tattaro cewa dabarar da matashin ya yi amfani da shi yana daidai da shahararriyar al'adar mutanen Afrika ta Kudu.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

thembelihlexoloci ya ce:

"Wannan irinsa na daban ne na sume a lokacin da ya yanke shawarar komawa ya kwanta bayan an jefe shi da kudi."

Zanele Maluleke956 ta ce:

"Ina zub da hawaye saboda idan aka bi al'ada yadda yake yana tsuma mani zuciya ❤️. Wannan ya yi kyau."

Kara karanta wannan

Ikon Allah: Bidiyon Yadda Wani Yaro Ya Dafi Babbar Waya Ya Koma Kamar Babban Oga Ya Ja Hankali

Ntsako Mandewo ya ce:

"Ina kaunar wannan bangare na sasantawa zan dade har sai na samu adadin kudin da ya yi mun saboda kanne mata na da muhimmanci sosai da daraja."

Senzi Zimu ta ce:

"Wannan ya tsuma raina saboda na san kanina na nan ya matsu ya ga wannan lokaci."

A wani labari na daban, wani magidanci ya cika da mamaki bayan matarsa ta zauna tana sharbar kuka wiwi saboda kawai ya bukaci da ta yi wankin kayanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel