Yadda Wata Caudediyar Budurwa Ta Ruga Aguje Bayan Ta Yi Wasan Barkwanci da Soja

Yadda Wata Caudediyar Budurwa Ta Ruga Aguje Bayan Ta Yi Wasan Barkwanci da Soja

  • Wani bidiyon yadda ta kwashe yayin da wata budurwa ta buga wasan barkwanci da Soja ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya
  • Budurwa ta tunkari sojan yana zaune yana hutawa ta mika masa takarda ɗauki da sakon suka ko a ce zagi
  • Bayan karanta abinda aka rubuta nan take Sojan ya fusata ya bi yarinyar da gudu kuma ya yi nasarar cafke ta

Wata caudeɗiyar 'yar Najeriya ta ruga da gudun tsiya don neman tsira bayan ta buga wani wasan barkwanci da Sojan Najeriya.

A wani Bidiyo da aka wallafa a shafin TikTok, budurwar ta je wurin sojan wanda ke zaune yana shan iska, ta bar wurin bayan ta miƙa masa takarda ɗauke da sakon, "Kai babban wawa ne."

Wasan barkwanci.
Yadda Wata Caudediyar Budurwa Ta Ruga Aguje Bayan Ta Yi Wasan Barkwanci da Soja Hoto: @asa_nwa
Asali: UGC

Ba tare da ɓata lokaci ba aka ga Sojan ya miƙe zumbur ya fizgo reshen bishiyar da yake zaune a inuwarta ya bi budurwar da gudu.

Kara karanta wannan

Ka latsa ni: Kyakkyawar budurwa ta tari wani dan Najeriya, ta nemi su fara soyayya

Bayan ta shiga hannun sojan ne budurwar ta fara masa cewa wasa ne ba ta yi nufin zaginsa bane.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bidiyon ya nuna yadda ta dinga rokon Sojan sannan ta kama kokarin wanke kanta ta hanyar nuna masa inda mai ɗaukarsu ya tsaya.

Mutane sun maida martani a soshiyal midiya

Tiko ya ce:

"Wato kina iya gudu bayan kin tsokani Soja, duk da sojan ya ɗauki lokaci wajen karyo bishiya amma sai da ya kamo ki."

Olasunkami ya ce:

"Lallai Allah ya cece ki, da ace namiji ne da jikinsa ya gaya masa don sojan nan ba yarda zai yi ba, karfin mata kenan."

Unknown Lincoln ya ce:

"Wannan sai ya tuna mun lokacin da nake ɗaukar bidiyon wasu dake ba hammata iska, kawai wani ya ce a kamo mai ɗaukar faɗan."

MC C10 yace:

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Kama Hayan Ɗaki 1, Ta Shirya Shi Tamkar 'Aljannar Duniya' Da Sabon Firinji, Talabijin Da Kayan Ɗaki

"Ya kenan da ace ta waiga ta hango mai ɗaukar bidiyon ya cika wandonsa da iska."

A wani labarin kuma Kare Ya Kama Uwar Gidansa Na Holewa da Saurayinta a Daki, Ya Ture Shi a Bidiyo

Wani kare ya kawo cikas yayin da uwar gidansa ta gayyaci sahibinta gida, suna zaune suna sumbatar juna a ɗakin hutu.

Ganin abinda ke faruwa, nan take karen ya hankade saurayin ya shiga tsakani don kare uwar gidansa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel