Ba Zan Yi Kewar Aso Rock Ba Saboda Cin Zarafi - Shugaba Buhari

Ba Zan Yi Kewar Aso Rock Ba Saboda Cin Zarafi - Shugaba Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa yana iya bakin kokarinsa don ciyar da kasar nan gaba amma wasu na raina fadi tashin da yake yi
  • Shugaban Najeriyan ya ce ba zai yi kewar fadar shugaban kasa ba idan ya sauka saboda cin zarafin da ake masa
  • Buhari ya zargi wasu da kokarin tsorata shi don samun abun da suke so ta kowani hali ba tare da bin hanyar da ta dace ba

Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba zai yi kewar fadar shugaban kasa ba sosai saboda ana yawan kushe shi.

Buhari ya bayyana cewa yana iya bakin kokarinsa na ganin ya inganta kasar nan amma hakan bai isa ba kuma wasu mutane basa godiya da hakan, jaridar Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

"Abin Da Ya Janyo Rasuwar Ƴaƴa Na 2", Buhari Ya Yi Magana Kan Wani Sirrinsa Mai Sosa Zuciya

Buhari da mutanensa
Ba Zan Yi Kewar Aso Rock Ba Saboda Cin Zarafi - Shugaba Buhari Hoto: Bashir Ahmad
Asali: Facebook

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a liyafar cin abinci da iyalai da aminansa suka shirya don murnar cikarsa shekaru 80, a ranar Juma'a 23 ga watan Disamba, rahoton Aminiya.

Da aka tambaye shi kan abun da zai yi kewa game da shugabancin Najeriya idan ya sauka daga mulki Buhari ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Anya zan yi kewar abubuwa da yawa. Ina ganin ana cin zarafina. Na yarda cewa ina iya bakin kokarina amma duk da haka ana raina kokarina.
"Saboda akwai mutane da suke ganin za su iya razana ni don samun abun da suke so maimakon bin ta tsarin da ya dace don samun duk abun da suke son samu. Kuma akwai wasu mutane da ke son nuna rabin wayo."

Ban taba yunkurin sake aure ba, Buhari

Kara karanta wannan

Kaico: A karon farko, Buhari ya yi martani kan ce masa da ake 'Jubril na Sudan'

A gefe guda, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya magantu a kan jita-jitan da aka ta yadawa a shekarun baya game da zargin cewa yana yunkurin sake angwancewa da wata.

Buhari wanda ya yi watsi da lamarin ya ce abu mai kama da haka bai taba faruwa ba kawai dai wasu ne suka kirkiri zance kuma aka yi nasarar yadata a tsakanin al'umma.

Shugaban kasar ya kuma ce lamarin ya girmama har ta kai wasu yan Najeriya sun yi dafifin zuwa babban masallacin Abuja suna jiran ganinsa domin a daura auren alhalin babu wani batu mai kama da haka daga bangarensa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel