Shugaban Kungiyar Gwagwarmaya ta Yarabawa ta Duniya Yayi Murabus
- Farfesa Banji Akintoye, shugaban gwagwarmaya na kungiyar Yarabawa ta Duniya, yayi murabus tare da mika ragamar kungiyar hannun mataimakinsa
- Kamar yadda sakatare janar na kungiyar ya sanar, Akintoye yayi murabus ne sakamakon shekarunsa da suka tafi tare da rashin karfin jiki na tsufa
- Ya sanar da murabus dinsa tun a taron kungiyar da aka yi a ranar 17 ga Disamban 2022 kuma masu ruwa da tsaki sun aminta da hakan
Shugaban kungiyar gwagwarmayar Yarabawa, Ilana Omo Oodua ta duniya, Farfesa Banji Akintoye, ya yi murabusu daga mukaminsa.
An tattaro cewa, murabus din Akintoye ya biyo bayan rikicin cikin gida da ya mamaye kungiyar.
Amma a takardar da ya fitar a ranar Alhamis ta sanar da murabus dinsa, Akintoye, babban sakataren kungiyar Tunde Amusat, yace shugaban ya mika ragamar mulkin kungiyar ga mataimakinsa, Farfesa Wale Adeniran.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Amusat yayi ikirarin cewa Akintoye ya mika ragamar mulkin ga Adeniran saboda shekarunsa da suka yi nisa da kuma rashin karfin jiki, jaridar Punch ta rahoto.
Kamar yadda Amusat yace, a taron da kungiyar Ilana Omo Oodua ta duniya tayi a ranar 17 ga Disamban 2022, an amince da murabus din Akintoye tare da tabbatar da Adeniran matsayin sabon shugaban kungiyar.
Ya kara da cewa, gyara kundin tsarin mulkin kungiyar wurin tabbatar da Adeniran matsayin sabon shugaban za a fitar da shi a taron da zasu yi a karshen shekarar nan na tantance mambobi masu rijista.
“Akintoye ya duba nagartar Adeniran kuma ya yaba masa kan hakurinsa da dukkan nau’ikan bata suna, zagi da batanci wanda aka yi masa a baya.
“Adeniran farfesa ne da yayi murabus kuma shi ne Kwamishinan ilimi na farko a jihar Osun. ‘Dan asalin Ile-Ife ne.”
- Takardar tace.
An kama Sunday Igboho a Kwatano
A wani labari na daban, shugaban ‘yan aware tare da assasa kasar Yarabawa, Sunday Igboho, ya shiga hannun jami’an tsaro a jamhuriyar Benin wacce ake kira da Kwatano.
An kama shi ne a filin sauka da tashin jiragen saman kasar yayin da yake kokarin tsallakewa ya shilla Turai da matarsa wacce take Baturiya.
Tuni aka jefa shi gidan yari tare da garkame shi inda za a yi shari’a.
Asali: Legit.ng