Mai Aikin Tura Sako Ya Bingire Da Barci Kan Babur Dinsa, Bidiyonsa Ya Yadu

Mai Aikin Tura Sako Ya Bingire Da Barci Kan Babur Dinsa, Bidiyonsa Ya Yadu

  • Wani mutum da ke aikin tura sako a babur ya bingire da barci a kan babur dinsa bayan ya faka a gefen hanya don samun nutsuwa
  • Bidiyon wanda shafin Sellout ya wallafa ya taba zukatan mutane da dama kuma mutum 129k ne suka kalle shi
  • Wasu masu amfani da TikTok sun bayyana cewa za su so tallafawa mutumin wanda a cewarsu ya wakilci masu kwazon nema

Wani mutumi ya wallafa bidiyon wani dan aike a babu wanda ya gaji matuka har ya bingire da barci a kan babur dinsa.

Wani mai amfani da sunan Sellout a TikTok ya wallafa bidiyon a ranar 17 ga watan Disamba don nuna yadda mutumin ya faka babur dinsa don samun hutu a gefen hanya.

Dan aike a babur
Mai Aikin Tura Sako Ya Bingire Da Barci Kan Babur Dinsa, Bidiyonsa Ya Yadu Hoto: TikTok/@theplvto
Asali: UGC

Sauran masu amfani da TikTok sun mamaye bidiyon da martani bayan ya yadu kuma an samu mutum 129k da suka kalle shi zuwa ranar 20 ga watan Disamba.

Kara karanta wannan

Kamar da wasa: Amarua ta ce ba za a daga bikinta ba, ta zo wurin biki da ciwo a kafa

Bidiyon dan aike a babur yana shakar bacci

A bidiyon mai tsawon sakan 19, an gano mutumin a kan babur dinsa yana sharar barci a gefen hanyar da ke fama da zirga-zirgan ababen hawa.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Zuwa yanzu ba a san sunan mutumin ko inda yake sana'ar tasa ba yayin da wasu masu amfani da TikTok suka ce suna son tallafa masa.

Wasu da suka yi martani kuma sun nuna damuwa game da tsaron lafiyar mutumin kasancewar ya yi barci ne a kusa da titi.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

@Omorio12 ya ce:

"Ya yi kokari don gudun hatsari yayin tuki."

@Remi lawal ta yi martani:

"Ya yi aiki da hankali. Na so ace za mu hada masa kudi don jin dadin bikin kirsimetinsa."

@Empire_Bigdaff ta ce:

"Jinjina ga dukkan masu fafutukar nema."

Kara karanta wannan

Bakon Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Daurin Itace, Bidiyon Ya Ba Jama'a Mamaki

@signature ta yi martani:

"Ya yi hikima...amma bai tsira ba. da kamata yayi ya bar hanya gaba daya."

@Apako Apako master ya yi martani:

"Ya sa na tuna da rayuwata ta baya."

Matashiya ta koka bayan cikin da take dauke da shi ya sauya mata kamanni

A wani labari na daban, wata matashiyar mata ta nuna takaicinta a fili kan yadda juna biyun da take dauke da shi ya sauya mata kamanni kamar ba ita ba.

A cikin hotunanta da ta wallafa, an gano lokacin da take budurwa kyakkyawa da ita inda a dayan kuma aka gano ta da katan hanci wanda juna biyun ne ya hura ta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng