Yadda Juna Biyu Ya Fitar Da Wata Kyakkyawar Mata Daga Hayyacinta, Bidiyon Ya Yadu
- Wata matashiyar mata mai juna biyu ta wallafa wani bidiyo daa ke nuna yadda jikinta ya sauya a lokacin da ta yi nauyi
- Matar maai suna Heyosato ta wallafa bidiyon a ranar Juma'a, 16 ga watan Disamba kuma mutum fiye da miliyan 7.3 sun kalle shi
- Wasu mata da suka fuskanci hana lokacin da suke da ciki sun bayyana ra'ayoyinsu a sashin sharhi
- Wata matashiya mai amfani da TikTok ta wallafa bidiyon yadda fuskarta ya sauya a lokacin da take da juna biyu.
Matar mai suna Hayosato ta wallafa bidiyon a ranar Juma'a, 16 ga watan Disamba kuma cikin gaggawa aka samu mutum miliyan 7.5 da suka kalla.
A bidiyon, Heyosato ta nuna yadda take da kyau kafin ta dauki ciki da kuma yadda fuskarta ya sauya a lokacin da take da juna biyu.
"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali
Bidiyon sauyawar da wata mai ciki ta yi
Bidiyon ya nuna cewa Heyosato na da fuska mai dan karan kyau kuma babu kuraje kafin ta samu ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai abubuwa sun sauya yayin da juna biyu ya yi kaca-kaca da ita har fuskarta ya kumbura ya yi suntum.
Hakazalika, hancinta ya kara girma a hoton kuma mata da dama a sashin sharhi sun ce irin haka ta faru da su.
Heyosato ta yiwa bidiyon take da:
"Zan yi kyau sosai da juna biyu, na matsu. Juna biyu dan kwalta ne."
Kalli bidiyon a kasa:
Martani daga masu amfani da TikTok
@Flowerchild92 ta ce:
"Nima haka na yi kama da bayan kwado."
@Kriaty ta ce:
"Zan yi ta fada da uban dana kullun."
@Ambar O'hara ta ce:
"Hanci na ya tashi kamar na yi dambe da Mike Tyson sau 3."
@Maricchi07 ta ce:
"Har yanzu ina kokarin gano dalilin da yasa juna biyu ke sa hancin mata yin girma haka. Ina ta ganin haka na faruwa."
Saurayi ya maka budurwarsa a kotu kan zagin matarsa ta sunna
A wani labarin kuma, wani magidanci ya gurfanar da budurwarsa a gaban alkali bayan ya zarge ta zagin matarsa ta gida.
Ya kuma zargi abokiyar sharholiyar tasa da yi masa barazana da wasu hotunan tsaraicinsa.
Nan take alkali ya ci ta tara inda aka bukaci ta biya shi kudi naira miliyan takwas.
Asali: Legit.ng