Bako a Wurin Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Kyautar Itace, Bidiyon ya Yadu

Bako a Wurin Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Kyautar Itace, Bidiyon ya Yadu

  • Wani abun ban dariya ya faru da wasu sabbin ma'aurata a wajen shagalin bikinsu yayin da suke zaune tare
  • Wani mutum ya jawo cece-kuce, inda ya taho da karfin hali ya gabatarwa ma'auratan icce a matsayin kyautarsa garesu
  • 'Yan soshiyal midiya sun yi martani game da kyautar mutumin, inda wasu suke jinjina irin basirarsa yayin da wasu suke ganin hakan ba abun kwarai bane

Akwai wani lokaci da aka samu rudani daga bisani dariya ta barke a wajen liyafar wani biki, bayan wani mutum ya gabatar da wata kyautar da ba a saba bada ta ga ma'aurata ba.

A wani bidiyo da yayi yawo a dandalin TikTok, mutumin ya isa inda ma'auratan suke, inda ya gabatar musu da kyautar Icce.

Amarya da Ango
Bako a Wurin Biki Ya Gwangwaje Amarya da Ango da Kyautar Itace, Bidiyon ya Yadu. Hoto daga TikTok/@butulet
Asali: UGC

Ma'auratan sun dara yayin da mutumin ya bukaci daukar hotuna dasu tare da iccen.

Kara karanta wannan

Yadda Al'umma Suka Hadu Suke Gasar Cin Abinci a Jihar Cross - RIver

Bidiyon ya yadu a kafafan sada zumuntar zamani inda wasu suka siffanta kyautar mutumin a matsayin abu na rashin kyautawa. Wasu kuma sun kwashi nishadi tare da yin tsokaci mai ban dariya.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Legit.ng bata gano takamaiman wurin bikin ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoton.

Jama'a sun yi martani

Tuni jama'a sun yi martani kan wallafar bidiyon. Ga wasu daga ciki:

user495679630804 ya ce:

"Meye ma'anar wannan iccen, a kowacce al'ada hakan na nufin wahala, tsanani da rashin sa a. Ba ma wani iccen ba fatan alheri bane."

dic*ky ya ce:

"Ni kam nayi imani da cewa daga zuciyarsa kyautar take. Taya murna shine babban abu a rayuwa."

winniewins 1 ta ce:

"Babu abun da ba zai iya faruwa ba a wannan duniyar."

Gena Igorot ta ce:

Kara karanta wannan

Aure a Kudancin Koriya: Al'adr Daure Kafafun Ango Ana Zugarsa da Bulala Cike da Nishadi

"Wannan kyauta ce mai matukar amfani garesu. Hakan na nuna dumama sabuwar rayuwar iyali."

ogelism 111 ya ce:

"Meye ido na bazai gani ba."

simon ya ce:

"Al'ada ita ce abu mafi karfi dake nuna ko waye mutum ina son hakan! kada kayi hukunci da kallon iccen. Waye zai iya fada min ma'anar iccen."

Halimatusadiya ta ce:

"Idan da nice ba zan amsa ba."

Duk cikin shagali, 'dan uwan ango ya bindige amarya

A wani labari na daban, 'dan uwan ango ya bindige amarya ana tsaka da shagalin bikinsu yayin da yake taya su murnar auren.

Lamarin ya faru ne kasar India inda amarya mai shekaru 24 tace ga garinku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel