Ohanaeze Ta Karyata Batun Kashe Yan Arewa 100 a Kudu Maso Gabas

Ohanaeze Ta Karyata Batun Kashe Yan Arewa 100 a Kudu Maso Gabas

  • Kungiyar Ohanaeze Ndigbo ta yi Allah wadai da rahoton da ke cewa an kashe akalla yan arewa 100 a yankin kudu maso gabas cikin mako daya
  • Sakataren labaran kungiyar Inyamuran, Alex Ogbonna, ya bayyana rahoton a matsayin kanzon kurege mara tushe balle makama
  • Ohanaeze ta yi kira ga kama wadanda suka kokan sannan ta bukaci hukumar tsaro da ta tabbatar da da ganin sun gabatar da hujjarsu kan rahoton

Kungiyar kare muradun Inyamurai na Ohanaeze Ndigbo ta yi watsi da rahoton da ke ikirarin cewa an kashe yan arewa fiye da 100 a yankin kudu maso gabas.

A cikin wata sanarwa da kakakinta, Alex Ogbonnia, ya saki, kungiyar ta bayyana lamarin a matsayin karya mara tushe balle makama, jaridar Vanguard ta rahoto.

Ohanaeze Ndigbo
Ohanaeze Ta Karyata Batun Kashe Yan Arewa 100 a Kudu Maso Gabas Hoto: The Guardian Nigeria
Asali: Facebook

Ohanaeze ta yi watsi da batun kashe yan arewa 100 a kudu maso gabas

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Hotuna yadda wata mata Musulma ta raba kudi, abinci da atamfa ga kiristocin Kaduna

Ogbonnia ya yi kira da a binciki rahoton sannan ya bukaci hukumomin tsaro da abun ya shafa su kama wadanda suka kokan don nuna hujja kan irin wannan ikirari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar Inyamuran ta bayyana cewa irin wannan ikirari na iya tayar da kasar sannan kuma cewa bai kamata a yi masa rikon sakainar kashi ba.

Ta kuma yi kira ga hukumomin tsaro da su tabbatar da kama wadanda suka yada zargin na karya.

Ogbonnia a cikin jawabin nasa ya bayyana cewa rahoton da ke ikirarin cewa yan awaren IPOB sun kashe akalla yan arewa 100 cikin mako guda yana da matukar damuwa, TVC News ta rahoto.

Rahoton ya nakalto Auwal Abdullahi Aliyu, jagoran kungiyar hadaka ta arewa yana umurtan direbobi daga yankin arewa da su guji zuwa kudu maso gabas.

Wani bangare na jawabin na cewa:

Kara karanta wannan

Wata Mata Tace Allah-Fa-Fir Bazata Karbi Sabon Kudi Ba, Sabida Jabu Ne

"Da farko, karya ne cewa an kashe akalla yan arewa 100 a yankin kudu maso gabas cikin makon jiya."
"Abu na biyu, Dr. Aliyu da ake magana a kai baya cikin shugabannin arewa mazauna kudu maso gabas kuma saboda haka baya da hurumin magana kan dangantakar da ke tsakanin yan arewa da mutanen kudu maso gabas.
"Abu na uku: Mutum zai fara tunanin manufar da ke tattare da irin wannan karya da yunkurin tada zaune tsaye cewa "akalla yan arewa 100 aka kashe a kudu maso gabas a cikin makon jiya.
"Abu na hudu: Bincike zai nuna irin bata sunan da hakan zai yiwa Najeriya a tsakanin kwamitin kasashe cewa an kashe mutum 100 cikin mako daya."

Ni zan lashe zabe a kudu maso gabas, Atiku

A wani labari na daban, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ya nuna karfin gwiwar kawo yankin kudu maso gabas a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: An Sake Samun Ibtila'in Fashewa a Babban Birnin Wata Jiha a Najeriya

Atiku ya nanata cewar zai doke Bola Tinubu na APC da Peter Obi na Labour Party a zaben shugaban kasa, cewa shine ya fi cancanta ya gaji Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel