Wata Musulma Ta Yi Rabon Kayayyakin Abinci da Zannuwa Ga Zawarawa Kiristoci a Kaduna

Wata Musulma Ta Yi Rabon Kayayyakin Abinci da Zannuwa Ga Zawarawa Kiristoci a Kaduna

  • Wata mata a jihar Kaduna ta bayyana wa duniya akwai zaman lafiya tsakanin Kirista da Musulmin Arewa
  • Ramatu Tijjani ta raba kayan abinci, kudi da atamfa ga mata zaurawa da marayu don yin bikin kirsimeti cikin koshin lafiya
  • Ba wannan ne karon farko da mabiya addinin Islama da Kirista ke tallafawa juna a lokutan bukukuwa ba

Jihar Kaduna - Yayin da kirsimeti ya matso kuma kayayyakin abinci suka yi tsada, wata mata Musulma, Ramatu Tijjani ta yi rabon kayan abinci, zannuwa da kyautar kudi ga kiristoci a jihar Kaduna.

A cewarta, ta shirya rabawa mata sama da 200 zaurawa kayayyakin rage radadi yayin da ake tunkarar wannan biki na kirsimeti, Tribune Online ta ruwaito.

Ta ce tana yin hakan ne domin kara kulla dankon zumunci tsakanin kiristoci da musalmai a Najeriya tare da wanzar da zaman lafiya.

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Kai Hari Sokoto, Sun Sheke Tsohuwa Mai Shekaru 120 tare da Wasu 5

Kaduna: Wata mata ta raba kayayyakin abinci ga kiristoci a Kaduna
Wata Musulma Ta Yi Rabon Kayayyakin Abinci da Zannuwa Ga Zawarawa Kiristoci a Kaduna | Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Ta kuma bayyana cewa, tana fatan wadannan kyaututtuka za su sanya farin ciki a fuskokin zaurawa da mazajensu suka mutu da marayun da suke kula dasu a lokacin bukukuwan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Yadda rabon ya kasance a wani coci

Ta yi wannan aikin ne a jiya Lahadi 18 ga watan Disamba a cocin Christ Evangelical and Life Intervention Ministry da ke Sabon Tasha, a jihar Kaduna.

A cewarta, ta fahimci irin wadannan zaurawa da 'ya'yansu marayu na fuskantar matsaloli da dama na rayuwa, don haka ta yanke shawarin taimaka musu.

Rahama ta bayyana cewa, ta dauki tsawon shekaru 10 ya zuwa yanzu tana taimakawa mata kiristoci zaurawa da kuma 'ya'yansu marayu.

Akwai zaman lafiya tsakanin Musulmi da Kirista

Hakazalika, ta ce tana yin haka ne domin nunawa duniya akwai zaman lafiya tsakanin Musulmai da Kiristoci a Arewacin Najeriya.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: An Sake Samun Ibtila'in Fashewa a Babban Birnin Wata Jiha a Najeriya

Hotunan da majiyoyi suka yada sun nuna lokacin da matar ke raba wadannan kayayyaki tare da yara da manya da ke kiranta ''Mama''.

Da yake martani game da wannan aikin kirki da Ramatu ta yi, shugaban cocin, Fasto Yahonna Buru ya yaba da irin kokarinta da kuma yadda take taimakawa gajiyayyu a jihar, rahoton Daily Nigerian.

Malamin na addinin Kirista ya ce, cocin ba zai taba manta tallafin kwafin littafin Injila guda 50 da Ramatu ta kawo cocin.

A shekarar da ta gabata an samu wasu Musulmai da suka dura wani cocin Kaduna domin halartar bikin Kirsimeti don nuna ana tare da juna cikin zaman lafiya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel