PDP: Damar Da Atiku Ke Da Shi Na Lashe Zabe a Kudu Maso Gabas Ya Fi Na Taurarin Arewa

PDP: Damar Da Atiku Ke Da Shi Na Lashe Zabe a Kudu Maso Gabas Ya Fi Na Taurarin Arewa

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiki Abubakar, ya bugi kirji cewa zai kayar da Bola Tinubu na APC da takwaransa na Labour Party a Kudu maso gabas
  • Atiku ya nuna karfin gwiwa yayin da yake jaddada cewa shi kadai ne dan takarar shugaban kasa da ya cancanta a zaben 2023
  • Charles Aniagwu, kakakin kwamitin yakin neman zaben PDP ne yayi furucin a Asaba yayin da yake martani ga gangamin jam'iyyar a Anambra

Delta - Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya fada ma takwarorinsa na All Progressives Congress (APC) da Labour Party (LP) yankin da zai lashe a zaben 2023.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya ce Bola Tinubu na APC da Peter Obi na LP ba za su iya kayar da shi ba a yankin kudu maso gabas, yana mai cewa shi ya saba lashe yankin, New Telegraph ta rahoto.

Kara karanta wannan

Tinubu ko Peter Obi? An Fadi Dan Takarar da Gwamna Wike Zai Mara Wa Baya Bayan Raba Gari da Atiku

Atiku, Tinubu and Obi
PDP: Damar Da Atiku Ke Da Shi Na Lashe Zabe a Kudu Maso Gabas Ya Fi Na Taurarin Arewa Hoto: Atiku Abubakar, Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Atiku ya ce yana da yakinin lashe wannan yankin tare da gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa a matsayin abokin takararsa, sannan cewa shine dan takarar shugaban kasa mafi cancanta.

Halin da ake ciki game da Atiki Abubakar, Bola Tinubu da Peter Obi game da zaben 2023

Sai dai kuma, dan takarar shugaban kasar bai yi watsi da damar da Tinubu da Obi ke da shi na tattara kuri'u a yankunansu ba amma dai ya bugi kirjin cewa kuri'un ba za su isa da har waninsu zai iya kayar da shi ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Charles Aniagwu, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na PDP, ya bayyana hakan a ranar Lahadi, 18 ga watan Disamba, yayin da yake martani ga gangamin kamfen din jam'iyyar a Anambra.

Jawabinsa ya zo kamar haka:

"Ba wai Atiku na magana da daukar alkawari bane kawai, damar fa yake da shi a kudu maso gabas da sauran yankuna a kasar sun fi na taurarin arewa kuma hakan ya samo asali ne daga nasarorinsa na baya."

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa za mu zabi Tinubu a matsayin shugaban kasa – Kiristocin Kudu

Aniagwu ya kara da cewa idan aka zabi Atiku a 2023, zai tattauna da kungiyar ‘yan awaren kudu maso gabas domin magance matsalolinsu, rahoton The Cable.

APC da PDP Sun Mutu a Najeriya, Kwankwaso

A wani labarin, Sanata Rabiu Kwankwaso, dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar NNPP ya bukaci yan Najeriya da su kuka da kansu idan suka sake zaben tumun dare a 2023.

Asali: Legit.ng

Online view pixel