Magidanci Ya Maka Budurwarsa a Kotu Kan Zagin Matarsa, An Biya Shi Tara Miliyan N8

Magidanci Ya Maka Budurwarsa a Kotu Kan Zagin Matarsa, An Biya Shi Tara Miliyan N8

  • Wani magidanci ya samu tarar naira miliyan 8 bayan ya maka budurwarsa a kotu kan zagin matarsa tare da kiran sunanta a yanar gizo
  • Wani lauya mai suna Egi Nupe ne ya wallafa labarin Twitter inda ya ce an kuma bukaci budurwar ta baiwa matar mutumin hakuri
  • Labarin ya yi fice inda ya samu 'likes' fiye da 1,700 bayan an wallafa shi a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba

Wani mai amfani da Twitter ya wallafa labari mai ban mamaki na wani mutum da ya maka abokiyar sharholiyarsa a kotu sannan ya samu naira miliyan 8 na tara da aka ci ta.

Wani lauya mai suna Egi Nupe ya wallafa labarin a ranar Alhamis, 15 ga watan Disamba kuma ya ja hankalin jama'a sosai.

Matashi, kudi da budurwa
Magidanci Ya Maka Budurwarsa a Kotu Kan Zagin Matarsa, An Biya Shi Tara Miliyan N8 Hoto: Colorblind Images LLC, Bloomberg and Charlotte Schildmeijer / EyeEm / Getty Images.
Asali: Getty Images

Egi Nupe ya ce mutumin da ake magana a kai ya maka budurwar tasa a kotu saboda ta zagi matarsa a soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

“Na Rasa Sukuni”: Dan Najeriya Ya Koka a Bidiyo, Ya ce Matar Da Ya Aura Ya Kai Turai Tana Sharholiya Da Maza

Labarin Mutumin da ya maka budurwarsa a kotu

Baya ga zagin da tayi, mutumin ya yi ikirarin cewa budurwar ta saki hotunan tsaraicinsa a soshiyal midiya ba tare da izininsa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kotun ta ci matar tarar naira miliyan 5 na fallasa tsaraicin mutumin da kuma wani naira miliyan 3 na zagin matarsa.

Egi Nupe ya ce kotu ta ba matashiyar umurnin fitowa dandalin soshiyal midiya don ba matar mutumin hakuri.

Kalli cikakken labarin a kasa:

Jama'a sun yi martani

@McSamsony ya ce:

"Dan Allah nuna ni ga wannan hukunci, wannan nasara ne a wurin da ya dace ga maza masu sharholiya kuma ina da su da yawa a matsayin kwastamomi."

@eyiteeonline ya yi martani:

"Budurwata bata isa ta aikata haka ba. Tana son haukacewa ne?"

@okiTwiTs ta ce:

"Na so wannan. Ya kamata yan mata su san matsayinsu a doron kasa."

Kara karanta wannan

"Ku Wuce Ɗaki": Wani Mutumi Ya Sunkuci Matarsa Yayin da Ta Kai Masa Ziyarar Bazata, Bidiyon Ya Ja Hankali

@dtch007 ta yi martani:

"Toh yanzu nawa ne ma matar tasa."

@MarvelChidi ta yi martani:

"A matsayina na mace idan ina da saurayi a wajen aurena na yi laifi?"

@SikiruTanimowo ta yi martani:

"Akwai matsala da zaran budurwa ta fara ganin kanta daya da Hajiya babba."

Magidanci ya koka kan halin matarsa da ya kai Turai, ya ce maza take bi

A wani labarin, wani magidanci dan Najeriya mazaunin Turai ya garzaya shafin soshiyal midiya don kokawa a kan halin matarsa.

Ya ce matar da ya aura da kudinsa a Najeriya sannan ya kaita Turai ta zama abun da ta zama domin dai maza take bi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel