Tinubu Ya Ziyarci Birnin Gwari a Kaduna, Ya Sha Alwashin Murkushe Yan Bindiga

Tinubu Ya Ziyarci Birnin Gwari a Kaduna, Ya Sha Alwashin Murkushe Yan Bindiga

  • Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya kai ziyarar jaje garin Birnin Gwari a jihar Kaduna gabannin zaben 2023
  • Tinubu ya sha alwashin kawo karshen ayyukan fashi da makami da ta'addanci a arewa idan har ya zama magajin Buhari
  • Sarkin Birnin Gwari, Mallam Zubairu Maigwari, ya nadawa Tinubu sarautar Dakaren Birnin Gwari kasancewarsa dan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci yankin

Kaduna - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Ahmed Tinubu, ya yi alkawarin shafe yan fashi da makami da yan ta'adda a Kaduna da sauran yankunan arewa idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Tinubu ya bayar da tabbacin ne a ranar Litinin, 12 ga watan Disamba yayin wata ziyara da ya kai Birnin Gwari na jihar Kaduna domin yiwa mutane jaje kan hare-haren da yan bindiga ke kai wa yankin, Channels TV ta rahoto.

Kara karanta wannan

Kowa ya huta: Atiku ya fadi yadda zai yi kungiyar ASUU idan ya gaji Buhari a zaben 2023

Tinubu a masarautar Birnin Gwari
Tinubu Ya Ziyarci Birnin Gwari a Kaduna, Ya Sha Alwashin Murkushe Yan Bindiga Hoto: The Nation
Asali: UGC

Da yake jawabi a fadar sarkin Birnin Gwari, Mallam Zubairu Maigwari, Tinubu ya yi ta'aziyya ga mutanen masarautar kan rashi da suka yi na rayuka da dukiyoyi sakamakon hare-haren da yan bindiga suka shafe shekaru suna kai masu.

Ya yi bayanin cewa ziyarar da ya kai Birnin Gwari don samun masaniya kan halin da yankin ke ciki ne kai tsaye ta fuskacin tsaro da tattalin arziki, yana mai alkawarin murkushe yan bindiga daga yankin idan ya zama shugaban kasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Ga ni tsaye a gabanku, yallabai, don fada maku cewa akwai babban rabo da ke tafe. Zaben ya kusa, mun sake basu sanarwacewa ba za mu yi kasa a gwiwa ba a kokarinmu na shafe yan bindiga. Zan iya baku tabbacin cewa wannan shine abun da za mu ba muhimmanci."

An nadawa Tinubu sarautar Dankaren Birnin Gwari

Kara karanta wannan

Tinubu Ya Gana Da Shugabannin Musulunci, Ya Daukar Masu Alkawara Idan Ya Ci Zaben 2023

A nashi bangaren, Sarkin Birnin Gwari ya jinjinawa dan takarar shugaban kasa na APC kan samun karfin zuciyar ziyartar yankin da ke fama da rikici, lamarin da ya bayyana cewa ba kasafai yake faruwa ba.

Domin nuna godiya, sarkin ya nadawa Tinubu sarautar Dakaren Birnin Gwari saboda kasancewarsa dan takarar shugaban kasa na farko da ya ziyarci yankin da ke fama da rikicin yan bindiga, rahoton The Nation.

Mota Tinubu ya bi zuwa Birnin Gwari

Tsohon gwamnan na jihar Legas ya bi hanya ne zuwa Birnin Gwari bayan an tsaurara matakan tsaro.

Dan takarar shugaban kasar ya samu rakiyar abokin takararsa, Kashim Shettima, Gwamna Nasir El-Rufai, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong.

Sauran sune gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, gwamnan Jigawa, Abubakar Badaru, na Kebbi Atiku Bagudu da kuma dan takarar gwamnan APC a jihar Kaduna, Sanata Uba Sani.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-dumi: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Babban Basarake Mai Martaba a Jihar Zamfara

Shugaban kasa a 2023: Kiristoci sun yiwa Tinubu addu'an samun nasara a jihar Oyo

A wani labarin, wasu kungiyoyin addinin kiristanci sun hadu a karshen makon jiya domin yin addu'a ta musamman kan nasarar Bola Tinubu a zaben 2023.

Wani basaraken yankin ya ce bai kamata lamarin addini ya shigo harkar siyasa ba domin ciyar da kasar gaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel