Wani Dan Najeriya Ya Janyo Cece-Kuce Yayin da Ya Kwashi Tsabar Kudi Dala Dubu 500 Zuwa Banki
- Hotunan wani dan Najeriya da ya kwashi kudade $500,000 (N220m) zuwa banki ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta
- Mutumin da ba a bayyana sunansa ba ana kyautata zaton ya kawo kudaden ne zuwa banki yayin da Najeriya ta sauya fasalin Naira
- Jita-jitan da ke yawo na cewa, kasar Amurka za ta daina amfani da wasu daga cikin kudadenta na ci gaba da jawo magana a duniya
Najeriya - Wani dan Najeriya ya cece-kuce yayin da ya dauko tulin kudade $500,000, da suka yi daidai Naira miliyan 220 zuwa banki domin ya ajiye.
Hoton mutumin da ba a bayyana wanene shi ba ya yadu a kafar sada zumunta, inda mutane da dama ke ta mamaki tare da rokon Allah su ma ya basu.
An dauki hoton ne a daya daga cikin bankunan kasar nan, wasu mutane sun shiga mamakin dalilin da yasa mutumin ya ajiye kudade masu yawa kamar wadannan.

Asali: UGC
Bai bayyana ko mutumin ya saba ka’ida da dokar adana kudi ta Najeriya ba kasancewar ya adana kudi da yawa gashi kuma ana karancin dala a kasar, lamarin da ya karya Naira.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Najeriya dai na ci gaba da kawo dokokin ajiye da cire kudi a kokarin da take na farfado da tattalin arzikinta.
Martanin jama’a
Wani yace::
"Kada ku yi masa hassada mana. Kuka san ko mai garkuwa da mutane ne, dan bindiga ko dan ta’adda? Su ne masu rike da kudade musamman daloli a yanzu.”
Wani kuma cewa ya yi:
“Ku ci gaba da bulayi. Kudaden da kuka sa wani ya ajiye muku a asusun da ya yi bacci kuma kuna umartarsa ya dauki hoton shaidar ajiye kudin.”
A kwanakin baya, yawaitar siyan daloli a kasar bayan fage na kadan daga cikin dalilan da suka darajar Naira ta yi kasa a duniya.
Wani mai sharhi a yi imani da cewa, yawaita boye dala ko kuma sauya Naira zuwa dala na ci gaba da cike kasuwannin bayan fage a kasar nan.
Abbas Yishau, wani dan jarida a gidan rediyon Now in Kano ya shaidawa Legit.ng cewa, da yawan masu boye kudaden nan sun shiga tsoron nan gaba za a daina amfani da wasu daga nau’in dala a duniya.
A makon nan gwamnan CBN ya gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari na Najeriya kan batun da ya shafi kayyade adadin kudaden da 'yan kasar za su iya cirewa a kowacce rana.
Asali: Legit.ng