Bayan Gwajin DNA Ya Nuna 'Ya'ya 5 Da Ta Haifa Ba Na Mijinta Bane, Mata Ta Magantu

Bayan Gwajin DNA Ya Nuna 'Ya'ya 5 Da Ta Haifa Ba Na Mijinta Bane, Mata Ta Magantu

  • Bayan shafe fiye da shekaru 30 da aure, wani magidanci ya hadu da abun al’ajabi a rayuwarsa game da yaransa
  • Gwajin DNA ya nuna cewa dukka yaransa guda biyar ba shine ya haifesu ba, amma matar tasa tana da ta cewa
  • A cewar wata matashiya da ta bayar da labarin, babban dan shekarunsa 32 yayin da karamin ke da shekaru 15

Bayan sama da shekaru 30 da aure, wani magidanci ya gano cewa dukkanin yaransa guda biyar ba shine yayi cikinsu ba.

A cewar wata matashiya mai suna @Meyeownboss wacce ta bayar da labarin a Twitter, mutumin mai shekaru 55 ya gano hakan ne bayan ya yi gwajin DNA.

Magidanci
Bayan Gwajin DNA Ya Nuna 'Ya'ya 5 Da Ta Haifa Ba Na Mijinta Bane, Mata Ta Magantu Hoto: FG Trade, Twitter/@Meyeownboss, @royalskegee
Asali: Getty Images

@Meyeownboss ta bayar da labarin wanda ya faru a gaske domin martani ga wani labari na mai wajen gwajin DNA, @royalskegee, wanda ya ce ya yiwa wasu ma’aurata da ke da yara uku gwaji kuma sakamako ya nuna ba mijin bane ubansu.

Kara karanta wannan

Yadda Gwamnatin Jihar Kogi Ta Gudanar Da Jana'izar Mutane 130 Da Babu Masu Shi

@Meyeownboss ta kara da cewa matar mutumin tana da ta cewa a lokacin da aka tunkare ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matar ta bayyana cewa dukka gwajin DNA da aka yi ba daidai bane. Ga yadda ta wallafa:

“Na dawo nan don fadin cewa na kalli wata hira da magidanci mai shekaru 55 wanda ya shafe fiye da shekaru 30 da aure da yara biyar, karamin shekarunsa 15 yayin da babban ke da shekaru 32…babu ko daya….na maimaita..babu ko daya da yake nasa. Da aka tunkare ta sai matar tace dukka gwajin dna din ba daidai bane.
“Na maimaita, ta ce, dukka gwajin DNA 5 da aka yi akwai kuskure.”

Jama'a sun yi martani

@Humanity_B ta ce:

“Na san wani da ke da yara 3 shima, dukkaninsu ba nashi bane. Yana a ganiyar shekaru 40 da doriya kuma yana neman mata ido a rufe, yana son yara saboda yana ganin an barsa a baya tsararrakinsa sun yi aure da yara sannan shi baida ko daya…”

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da 'yan bindiga suka tsare uwa da jaririnta, suna neman fansan miliyoyi

@lodiedodie14 ta ce:

“Ina da wata kawa haka…babu ko daya daga cikin nata da yake na saurayinta. Karamin yaron ya fito don haka sai suka yi gwajin DNA. Sai abokinsa ya ce yaya za a yi ka san ko sauran biyun naka ne? ya yi masu gwaji. Suma ba nasa bane. Na zata zai kashe kansa.”

@EiinsBin ya ce:

“Ya kamata kotuna su saka doka game da irin wadannan abubuwan. A haramta haihuwar yara da wani sannan ka yi ikirarin wani daban ne ke da su ba tare da saninsu ba."

Mata Da Kudi: Yadda Yan Mata Suka Mato Kan Matashi Dan Tsurut Da Ke Tuka Dankareriyar Jeep Cikin Salo A Bidiyo

A wani labarin, jama’a sun yi cece-kuce bayan bayyanar bidiyon wani mutum dan yana nuna yadda yake iya tuka tsadaddiyar babbar motarsa duk da kasancewarsa dan tsurut.

Mutumin mai suna Katuosis Babayao ya yada bidiyon don cire kokwanto a zukatan mutanen da ke tunanin ba zai iya tuki ba ko kuma wadanda ke mamakin ya yake tuka motar.

Kara karanta wannan

Gwajin DNA: Bayan Shekaru 20 Da Aure, Liktita Ya fadawa Magidanci Dukkan 'Yayan Matarsa 5 Ba Nasa Bane

A cikin bidiyon, Babayao ya nuna yadda aka kera masa kujerarsa na zaman tuki zuwa na musamman. Kujerar ta fi ainahin kujerun motoci da aka saba gani tsawo domin bashi damar ganin hanya da kyau.

Asali: Legit.ng

Online view pixel