Tsohuwa Ta Yi Tattaki Daga Turai Zuwa Najeriya Don Haduwa Da Sahibinta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce

Tsohuwa Ta Yi Tattaki Daga Turai Zuwa Najeriya Don Haduwa Da Sahibinta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce

  • Wata dattijuwar mata mazauniyar Turai ta samu cikar burinta yayin da ta yi ido hudu da masoyoyinta
  • Matar ta shigo Najeriya don haduwa da saurayinta wanda take yiwa lakabi da 'babi' sannan ta ayyana cewa soyayya lallai soyayya ce
  • Bidiyon tafiyarta da lokacin haduwarsu da dogon saurayinsa ya haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya

Wata dattijuwar mata ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta iso Najeriya don ganin sahibin ranta.

Da ta garzaya dandalin TikTok, ta wallafa bidiyon isowarta filin jirgin sama na Najeriya, inda ta ayyana lallai soyayya soyayyace.

Masoya
Tsohuwa Ta Yi Tattaki Daga Turai Zuwa Najeriya Don Haduwa Da Sahibinta, Bidiyon Ya Haddasa Cece-kuce Hoto: TikTok/@blessedtamma
Asali: UGC

Ta wallafa wani bidiyo da ya hasko ta a wajen gyaran gashi, tana mai bayyana cewa saurayinta ne ya sa hakan ya faru.

Matar wacce ke cike da farin ciki ta kuma hadu da wasu yara a masaukinsa. Ta kuma wallafa bidiyoyinsu suna daukar salfie da kuma tafiya tare.

Kara karanta wannan

Aure Daɗi: Bidiyon Yadda Wata Mata Ta Maƙale Wa Mijinta, Ta Hana Shi Rawar Gaban Hantsi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jama'a sun ji mata tsoro sannan sun nuna shakku kan gaskiyar mutumin, suna masu bata shawarar ta jira kwanaki 90. Ta mayar da martani da:

"Bana bukatar saka ido sosai a kan soyayyata saboda kwanaki casa'in."

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

NurseIzzy ta ce:

"A matsayina na mamba a nahiyar Afrika, na fahimci fafutukar komawa gida sannan na fahimci abun da dan uwana ke kitsawa."

2blessed2bStressed_1 ta ce:

"A zahirin gaskiya, dukkanmu muna so a so mu sannan a wasu lokutan yana makantar da mu kan abubuwa da yawa."

Vee ta ce:

"Dan Allah kawai ki kai ziyara kawai saboda zai kare cikin hawaye idan kika kawo shi nan."

Matashi ya hadu da sharrin 'late comer' bayan budurwarsa ta auri wani daban

A wani labarin, wani matashi ya shiga dimuwa da damuwa bayan budurwar da ya shafe tsawon shekaru yana fadi tashi a kanta ta auri wani na daban.

Kara karanta wannan

Wata Mata Ta Biya Kudin Jirgi Daga 'Kasar Waje Dan Ganin Saurayinta

Ko kafin ya samu labarin aurenta, sai da ta kira shi cewa kanwarta zata yi aure sannan ta saka shi a gaba yayi mata siyayya harda gudunmawar kudi ya bayar domin a baiwa mai auren.

Kwatsam sai ya gano cewa ai aurenta za a yi sabanin yadda ta sanar da shi tun farko.

Asali: Legit.ng

Online view pixel