A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

A Dare Daya, CBN Ya Kawo Tsarin Da Mutane Miliyan 1.4 Za Su Rasa Aiki – Kungiya

  • Victor Olojo yana ganin an fito da tsarin rage kudin da ke yawo, amma a karshe illa zai yi wa Najeriya
  • Shugaban kungiyar masu sana’ar POS na kasar nan yace CBN zai jawo mutanensu su rasa hanyar abinci
  • Masana tattalin arziki sun ce tsarin zai jawo rashin ayyukan yi da karin wahalar kasuwanci a karkara

Abuja - Shugaban kungiyar masu sana’ar POS a Najeriya, Victor Olojo, yana tsoron irin mummunan tasirin da tsarin takaita cire kudi zai yi masu.

Mista Victor Olojo ya yi wannan bayani sa’ilin da ya tattauna da Punch a karshen makon jiya.

Shugaban kungiyar AMMAN ya yaba da kokarin da bankin CBN yake yi na farfado da tattalin arziki da kawo tsare-tsare domin rage tashin farashi kaya.

Amma Olojo ya koka da cewa akwai mutane fiye da miliyan 1.4 da suke sana’ar POS a Najeriya, kuma tsarin zai iya jawowa su rasa hanyar samun abinci.

Kara karanta wannan

Dan Ba Kara Zaben APC A 2023: Mun Zabi Buhari Wahala Ta Kusan Kashe Mu, iInji 'Yan Arewa

'Yan POS za su nemi alfarma a CBN

A cewar shugaban AMMAN, idan aka yi bincike, za a gane masu sana’ar POS sun saukaka rayuwar al’umma wajen samun kudi ba tare da zuwa baki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Oloja yace a game da batun cire kudi, ba za su ce bankin CBN yayi watsi da shirin ba, amma za su nemi alfarmar a ba su damar cire fiye da N20, 000 a rana.

Injin POS
Kudi da POS Hoto: www.akahinews.org
Asali: UGC

N6.4tr ake lissafin sun bi ta na’urorin POS a shekarar 2021, idan aka ce N100, 000 kurum masu sana’ar za su iya cirewa a mako, an tsaida kasuwancinsu.

Shiyasa Oloja yake da ra’ayin tsarin na CBN zai kara kawo matsalar rashin ayyukan yi.

A lokacin da aka shigo da karbar kamasho idan aka sa kudi a banki, ‘yan AMMAN sun nemi alfarma aka janye kamashon kan abin da bai kai N10, 000 ba.

Kara karanta wannan

Emefiele zai kashe mu: Jam’iyyun Siyasa Sun Yi Wayyo da Dokar Takaita Cire Kudi

Tasirin sabon tsarin CBN

Wani rahoto da muka samu ya nuna baya ga ‘yan POS, kananan ‘yan kasuwa za su koka da tsarin domin zai kara yawon masu zaman banza a kasar nan.

Sannan tsarin zai iya yin sanadiyyar da fashi da makami zai karu saboda rashin manyan kudi. Manyan ciniki a kauyukan Najeriya zai zo da kalubale.

Jam'iyyu sun koka

Kun ji labari jam’iyyun siyasan da za su shiga takara a 2023 sun ce rage kudin da za a cire a banki zuwa N20, 000 zai nakasa su wajen samun dukiyar kamfe.

Jigo a PDP, da wani ‘Dan takaran Shugaban Kasa Jam’iyyar SDP da kuma Kakakin SDP na kasa sun nuna ba su goyon bayan Gwamnan CBN a kan wannan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel