Zai Yi Wahala Ace Anyi Magudin Zabe Inji Shugaba Muhammadu Buhari

Zai Yi Wahala Ace Anyi Magudin Zabe Inji Shugaba Muhammadu Buhari

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa lalle za'ai sahihin zabe ba tare da magu'di ba
  • Kasa da wata 3 da gabatar da babban zaben Nigeria hukumar zabe ta nanata kudirinta na yin sahihin zabe
  • Tsohon kwamishina a hukumar zabe Igini, yace akwai tabbacin yin sahihin zaben a Nigeria a 2023 wanda ba'a taba irinsa ba

Abuja: A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nanata kudirin tabbatar da gaskiya da adalci a zaben 2023 mai zuwa, yana mai cewa ba zai bari a yi magudi ba ta kowace fuska ba.

buhari
Zai Yi Wahala Ace Anyi Magudin Zabe Inji Shugaba Muhammadu Buhari Hoto: Leadership
Asali: UGC

Shugaban ya yi wannan jawabi ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar dattawan Afrika ta Yamma, karkashin jagorancin tsohon shugaban kasar Saliyo, Dr Ernest Bai Koroma, a fadar shugaban kasa.

Kara karanta wannan

A Karshe ‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Yi wa Duniya Bayanin Yadda Ya Mallaki Dukiyarsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na gode da yarda kuka amince mana, kuma kuke hidima ga wannan yankin namu" in ji shugaba Muhammadu Buhari

Buhari ya bayyanawa tawagar irin yadda akai zabubuka a jihohin Anambra, Ekiti da Osun, a matsayin abin da ke nuni da cewa gwamnatin tarayya za ta bai wa mutane damar zabar shugabannin da suke so.

Leadership ta rawaito cewa Buhari bai gushe ba sai da ya kara tabbatar da kudirin aiwatar da sahihin zabe, inda yake cew:

“Muna tabbatar da Jama'a su zabi wanda suke so, a kowace jam'iyya. Ba za mu bari wani ya yi amfani da kudi da ‘yan daba don tsoratar da jama’a ba.
’"Yan Najeriya suna da ilimi, suna da hikima, kuma sun san cewa gara a tattauna da a dauki makamai".

Su Waye Suka Kaiwa Buhari Ziyarane Har Yake Wannan Maganar?

Kara karanta wannan

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

Daga cikin shugabannin da shugaba buhari ya karbar a fadar sa sun hada da Tsohon shugaban kasar Koroma wanda ya jagoranci tawagar sai Fatoumata Tambajang, tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Gambia.

A cikin tawagar akwai Dr Mohammed Ibn Chambas, tsohon wakilin na musamman ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, da Ann Iyonu, babban darakta a gidauniyar Goodluck Jonathan.

Yayin Ziyarar tasu sun sanar da Buhari cewa sun gana da masu ruwa da tsaki a jam’iyyu, kungiyoyin farar hula, da hukumar zabe mai zaman kanta da dai sauransu.

Tawagar ta yabawa shugaba Buhari kan yunkurinsa na tabbatar da anyi sahihin zabe a 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel