A Karshe ‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Yi wa Duniya Bayanin Yadda Ya Mallaki Dukiyarsa

A Karshe ‘Dan Takaran APC, Tinubu Ya Yi wa Duniya Bayanin Yadda Ya Mallaki Dukiyarsa

  • Asiwaju Bola Tinubu ya wanke kan shi daga zargin da ake yi masa na mallakar kudi ta muguwar hanya
  • ‘Dan takarar shugaban kasan yace a duk Gwamnonin da suka shude, babu wanda aka yi ta bincike irinsa
  • Tinubu yake cewa ba a same shi da laifi ba domin da hannun jari da gadon gidaje ya tara dukiya a Duniya

London - Asiwaju Bola Tinubu mai takarar zama shugaban Najeriya a karkashin jam’iyyar APC ya yi magana a game da silar arzikinsa a Duniya.

Asiwaju Bola Tinubu yayi wannan bayani ne a lokacin da BBC tayi hira da shi a garin Landan, kasar Ingila, bayan gabatar da jawabi a Chatham House.

‘Dan takarar shugaban kasar yace a duk tsofaffin Gwamnonin jihohi da aka yi, babu wanda aka tasa da bincike kamarsa, amma ba a gano laifinsa ba.

Kara karanta wannan

Na Shirye Kazancewa a Siyasar 2023, Dan Takarar Shugaban Kasa Na Sahun Gaba Ya Fusata

Da aka nemi Bola Tinubu ya yi bayanin yadda ya samu tulin dukiya, Daily Trust tace ‘dan takaran ya nuna siyasa ta sa ake yawan masa tambayar nan.

Tambaya ko zargi?

An ji ‘dan siyasar yana kokawa da yadda aka yi masa tambayar, kamar ana zarginsa da laifi.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Tsohon Gwamnan na jihar Legas ya zargi abokan gaba da yi masa bakin-ciki da hassada, yace ya narka kudi ne a kasuwancin da suka kawo masa riba.

Bola Tinubu
Bola Tinubu da Ministan Birtaniyya Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Irin na Warren Buffet Tinubu ya yi

Shin su ba su son dukiya ne? Idan su ba makiyan dukiya ba ne, kasuwanci suna kawo riba. Na bada misali da Warren Buffet.
Yana daga cikin manyan masu kudin Amurka da Duniya. Ya fara da sayen hannun jari, ya gaji gidaje. Ina jawo kaya suyi daraja.

Kara karanta wannan

Shinkenan ta takewa Tinubu, 'yan jiharsa su bayyana dan takarar da za su zaba ba shi ba

Ba na musanya dukiya ta, babu tsohon Gwamnan da aka yi shekaru takwas ana bincika iri na, har zuwa 2007 da na bar karagar mulki.
Har yau kuma ga ni nan, kuma ban taba karbar wani mukani a gwamnati ba.” - Bola Tinubu

Baitul-malin jihar Legas

Da aka bijiro da zargin cewa harajin da ake biya a Legas suna shigowa aljihunsa, The Cable ta rahoto Tinubu yana mai musanya batun da cewa hassada ce.

Tinubu yace IMF ta binciki kudin da ke shiga da fita a Legas, kuma babu hujjar da ke nuna yana cin dukiyar al’umma, yace hassadar ‘yan adawa ce kurum.

EFCC tana neman 'Dan takaran Sanata

Rahoto yace ana shari’a da AbdulKareem AbdulSalam Zaura wanda shi ne ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar APC a zaben 2023.

AbdulKareem Zaura wanda aka fi sani da A.A Zaura ya ki zuwa amsa zargin da ake yi masa na satar $1.3m a kasar Larabawa, don haka EFCC ta fara cigiyarsa.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Atiku, Obi, Kwankwaso Suka Fada a Taron 'Yan Takaran 2023

Asali: Legit.ng

Online view pixel