Rikicin Duniya: ‘Dan Haya Ya Maka Maigidan Haya a Kotu Kan Taki Siyar Masa da Gidanta

Rikicin Duniya: ‘Dan Haya Ya Maka Maigidan Haya a Kotu Kan Taki Siyar Masa da Gidanta

  • Babbar kotun tarayya a Legas tayi watsi da karar wani tsohon sojan sama mai suna Onitiju wanda ya kai mai gidan hayansa kan siyar da gidanta da tayi
  • Ya sanar da kotun cewa da shi aka fara ciniki kuma ya daga kadarorinsa har biyu ya siyar don siyan gidan benen mai dakuna hudu
  • Ya zargi mai gidan da kin bashi lambar asusun bankin da zai tura kudin sannan ta nemi wan tsohon sojan kasa ta siyar da gidan kan N135m

Legas - Wata babbar kotu dake zama a Legas tayi fatali da karar wani Ademola Onitiju, ‘dan haya wanda ya maka mai gidan da yake ciki kotu kan ta siyarwa wani gidanta ba shi ba.

Maigidan Haya a kotu
Rikicin Duniya: ‘Dan Haya Ya Maka Maigidan Haya a Kotu Kan Taki Siyar Masa da Gidanta. Hoto daga TheCable.ng
Asali: UGC

A shekarar 2021, Onitiju wanda soja ne mai ritaya kuma lauya, ya kai Theodosia Ogunnaike, wacce ta mallaki gidan bene mai daki hudu dake rukunin gidajen Dolphin a Ikoyi, gaban kotu kan ta siyarwa wani gidan bayan sun fara ciniki, jaridar TheCable ta rahoto.

Kara karanta wannan

Budurwa Ta Yi Bidiyon Wani Gida Mai Daki 1 Da Za a Bayar Haya Kan N1m A Abuja, Jama'a Sun Yi Martani

‘Dan hayan mai shekaru 59 wanda ya fara zama a gidan a watan Disamban 2015, yace shi aka fara yi wa tallar gidan amma bai biya a take ba.

Onitiju yace da farko an bukaci ya biya N170 miliyan amma yace zai biya N90 miliyan wanda mai gidan tace bata yarda ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon sojan saman yace a yayin cinikin, ya siyar da kadarorinsa biyu domin ya samu kudi har N135 miliyan wanda suka sasanta a kai.

Yace ya bukaci lambar asusun bankinta domin ya biya kudin amma aka hana shi har sai da aka siyarwa wani Samuel Dare, Soja mai mukamin kanal da yayi ritaya.

TheCable ta rahoto cewa, Onitiju ya amsa cewa wacce yake karar bata bukaci ya siyar da kadarorinsa ba,

“Amma sun yi hakan da dabara lokacin da suka ce sai ya siya gidan kan N135 miliyan.”

Kara karanta wannan

Kungiyar ASUU Na shirin yin Zanga-Zangar Sabida Kin Biyanta Albashi Da Gwamnatin Tarayya Tayi

Ya kara da sanar da kotun cewa bashi da wata shaidar inda N135 miliyan dinsa ta shige.

‘Dan hayan ya bukaci kotun da ta kwace gidan tare da warware ciniki da tsohon sojan.

Daga bakin mai gidan hayan

Ogunnaike, matar da mijinta ya mutu tace gidan na diyarta ne amma ita ke kula da shi. Mai gidan tace Onitiju yana biyan kudin haya N4.5 miliyan a kowacce shekara a asusun bankinta kuma ba a taba kara masa kudin haya ba saboda alaka mai kyau da suke da ita.

Mai gidan tace Onitiju aka fara yi wa tayin gidan amma bashi da kudin biya.

Daga nan ta fasa siyar masa bayan yace N90 miliyan ko N100 miliyan zai iya biya, daga nan aka tallata gidan a waje.

A hukuncin ta na ranar 20 ga watan Yunin 2022, Bola Okikiolu Ighile, alkalin kotun tace shaidun da aka bayyana a gaban kotu baya goyon bayan kowanne rage radadi da yake bukata kuma karar bata da makama. Daga bisani aka yi watsi da ita.

Onitiju kuwa ya ki hakura inda a halin yanzu ya daukaka kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng