Budurwa Ta Bazama Neman Haya a Abuja, An Kaita Wani Gida Mai Daki 1 Da Za a Biya N1m

Budurwa Ta Bazama Neman Haya a Abuja, An Kaita Wani Gida Mai Daki 1 Da Za a Biya N1m

  • An kai wata budurwa da ke neman haya a Abuja wani gida mai daki daya da lalataccen hanya kan miliyan N1
  • Cike da takaicin lamarin, ta yi bidiyon yadda tafiyar ta kasance don nunawa mutane wahalar da ta sha
  • Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyon sun yi kokarin sama mata mafita na inda zata samu gida mai kyau

Abuja - Wata matashiya yar Najeriya, preciousubani_, wacce ke neman haya a Abuja, ta wallafa wani bidiyo da ke nuna halin da ta shiga lokacin da take neman gida.

Ta bayyana cewa wani dillali ya nemi ta zo ta duba wani gida mai daki daya da za a bayar da haya kan naira miliyan 1. Kai tsaye matashiyar ta tafi wajen cike da murna.

Budurwa mai neman gidan haya
Budurwa Ta Bazama Neman Haya a Abuja, An Kaita Wani Gida Mai Daki 1 Da Za a Biya N1m Hoto: TikTok/@preciousubani
Asali: UGC

Lalataccen hanya zuwa gidan haya na N1m

Kara karanta wannan

Tsananin yunwa: Bidiyon mata 'yan Arewa na wawar shinkafa a kan tunkuya ya tada hankali

Abu daya da bai mata ba shine cewa hanyar da zai sada mutum da gidan bai da kyau ko kadan.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A lokacin da ta isa sabon gidan, sai ga cewa zata dunga hawa wani dogon saman bene kafin ta isa dakinta.

Mutane da dama da suka yi martani ga bidiyonta sun bayyana cewa neman gida a Abuja akwai matukar wahala.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani

Ayobillion ya ce:

"Don samun gida mai kyau ki duba wajajen Lokogoma, apo, gudu, ki fadama dillalan su mayar da hankali kan wadannan yabkunan. Za ki samu gidan kasa da miliyan kuma mai kyau."

Jessica_byankss ta ce:

"Kina da hakuri, da na juya tun daga farkon hanyar. Gidan babu laifi amma hanyar ba nan bane."

waiz_man ya ce:

"A iya shekaruna a Abuja, ban taba sanin cewa za a iya samun wurare da irin hanyoyin nan ba."

Kara karanta wannan

Matar Aure Ta Kama Mijinta Na Rage Zafi Da Wata Yar Magajiya, Bidiyon Matakin da Ta Dauka Ya Girgiza Mutane

Dynamic Micky ya tambaya:

"Yaya nauyin aljihunki kuma ta ina kike so?"

Ta amsa:

"N1m. Koina ya dai kasance kusa da cikin gari."

remispeaks ya ce:

"Gara ki zo wuye. Akwai tsaro sosai a nan kuma kina da tabbacin wuta da ruwa.

Matashi dan shekaru 16 ya mallaki motarsa ta farko

A wani labarin, wani matashi mai shekaru 16 ya gwangwaje kansa da wata tsadaddiyar mota da ya siya da kudinsa.

Yayan matashin ne ya garzaya shafin yanar gizo domin taya dan uwan nasa murna inda ya jaddada lallai kudi babu ruwansa da shekarun mutum.

Asali: Legit.ng

Online view pixel