Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde, Yayi Murabus

Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde, Yayi Murabus

  • Kwamishinan ilimi na jihar Gwamna Bala Muhammadu, Dakta Aliyu Usman Tilde ya yi murabus daga mukaminsa a jihar Bauchi
  • Dakta Tilde ya bayyana cewa wani aiki ne da ke matukar bukatarsa yasa ya ajiye mukamin da yayi sama da shekaru uku yana rike da shi
  • Tilde yayi godiya ga Allah da ya daga masa tare da gwamna da ya bashi damar aiki a kasan shi da kuma jama’ar Bauchi da ya mulka

Bauchi - Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi, Dakta Aliyu Usman Tilde, yayi murabus daga mukaminsa na majalisar zartarwa ta jihar.

Aliyu Usman Tilde
Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Dakta Aliyu U. Tilde, Yayi Murabus. Hoto daga leadership.ng
Asali: UGC

Tilde wanda ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook, yace tun farko ya turawa Gwamna Bala Muhammad takarda inda yake bukatar amincewa ya bar shi ya amsa kiran wasu wadanda ke matukar bukatar taimakonsa.

Kara karanta wannan

Bayan Shan Lugude da Gurfana a Kotu, Dalibin da ya Zolaya Aisha Buhari ya Koma Makaranta

Tilde yace:

“Wannan shi ne addu’a ta bayan na bar ofis a ranar Alhamis da ta gabata bayan na rubuta wasika zuwa ga Gwamna Bala Muhammad don ya bar ni in amsa kiran wasu makusanta dake bukatar taimakona.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Mintuna kadan da suka gabata a yau 5 ga watan Disamban 2022, na samu wasika daga sakataren gwamnatin jiha inda yake bayyana cewa an sahale min.
“A cikin wasikar, sakataren ya aiko da godiyarsa Mai Girma Gwamna kan gudumawar da na bai wa bangaren ilimi tare da yi min fatan alheri a abubuwan da zan yi nan gaba.”

Tilde ya sanar da cewa wa’adinsa na zama kwamishinan ilimi a jihar ya zo karshe inda ya kara da cewa:

“Ina farin cikin ganin karshen abinda zan ce ya kasance shekaru masu amfani kuma zan cigaba da godiya ga Allah da ya tsaya min har mintin karshe.

Kara karanta wannan

Nagode Mama: Aminu Adamu ya Bada Hakuri a Fili, Yayi Alkwari Zai Gyara Halinsa

“A dole wannan ayar ta zo zuciyata yayin da nake duba hotunana a ofishina. Ina fatan Allah ya kasance tare da ni a sabon aikin da zan fara.”

Ya mika godiyarsa ga Gwamnan jihar da jama’ar jihar Bauchi da suka bashi damar zama kwamishina na tsawon shekaru uku.

Kwamishina a Zamfara yayi murabus

A wani labari na daban, Alhaji Surajo Maikatako, kwamishinan lamurran aikin hajji yayi murabus.

A Sani taron ‘ya’yan jam’iyyar APC, Maikatako ya bayyana cewa yana da yakinin cewa jam’iyyar APC zata lashe zaben 2023 a jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel