Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle

Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle

- Alhaji Sirajo Maikatako, Kwamishinan aikin hajji na jihar Zamfara ya yi murabus

- Ya bayyana hakan ne yayin yi wa 'yan jam'iyyar APC jawabi a ranar Alhamis a babban birnin jihar

- A cewarsa, yana da yakinin jam'iyyar APC ce za ta yi nasarar lashe zaben 2023 da za a yi a jihar

Kwamishinan aikin hajji, Alhaji Sirajo Maikatako, ya yi murabus. Ya bayyana hakan ne a wani taron 'yan jam'iyyar APC da aka yi a Gusau ranar Alhamis, Daily Trust ta wallafa.

Ya bayyana yakininsa inda yace jam'iyyar APC ce za ta lashe kaf kujerun jihar a zaben 2023, har yana cewa ya yi aiki ne karkashin jam'iyyar PDP a matsayin shugaba ba dan siyasa ba.

"Ina farin cikin sanar da canja shekata daga shugabanci a karkashin jam'iyyar PDP. Na yi hakan ne don nuna matukar goyon baya ga shugabana a harkar siyasa, Sanata Kabiru Marafa don samun wanzuwar kwanciyar hankali da hadin kan jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Kar ku zama sakarkaru, ku bai wa kanku kariya daga 'yan bindiga, Minista ga 'yan Najeriya

Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle
Kwamishina a Zamfara yayi murabus, ya ce APC za ta kwace kujerar Matawalle. Hoto daga @daily_trust
Asali: UGC

"Ina so in yi kira ga gwamnatin PDP ta jihar nan da ta guji siyasar tashin hankali da rikici. Ina sa ran 'yan PDP da sauran 'yan jam'iyya da su taya mu a matsayin 'yan APC murnar samun nasara.

"Muna kira ga gwamna Bello Matawalle da ya fuskanci abinda ya kawo shi kan mulki don samar da abubuwan da suka dace. A dakata har lokacin siyasa yayi," a cewarsa.

Maikatako ya shawarci kungiyar da ta guji yada labaran bogi ko munanan maganganu a kafafen sada zumuntar zamani don samar da kwanciyar hankali da zaman lafiya tsakanin 'yan jam'iyyu daban-daban.

"Daga yau, ina shawarar ku da kada ku kuskura ku kula wanda ya soki Marafa ko wani babba a jam'iyyarmu a kafafen sada zumuntar zamani.

"Mu cigaba da yiwa shugaban APC, Alhaji Abdul'aziz Yari addu'a don ya samu nasarar zama shugaban jam'iyyar APC na kasa," a cewarsa.

KU KARANTA: Hotunan wakilan FG, IGP da wasu jiga-jigai da suka kai ziyara Niger bayan sace dalibai

A wani labari na daban, wata mummunar gobara ta yi ajalin wani jariri a wani sansanin 'yan gudun hijira dake wuraren titin Mafa a cikin Maiduguri jihar Borno a ranar Talata.

Ganau sun tabbatar da yadda lamarin ya faru da misalin 7:30am na safiya a wani bangare na sansanin amma an samu nasarar kashe gobarar cikin karamin lokaci.

A cewar ganau din: "Wata gobara ta barke da misalin 1pm kuma ta yi sanadiyyar kone tanti da dama dake sansanin."

Wani jariri ya kone kurmus sannan wasu manya biyu sun kone kamar yadda ganau din ya tabbatar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel