Wani Babban Sarki Mai Shekara Sama da 100 a Arewacin Najeriya Ya Rasu

Wani Babban Sarki Mai Shekara Sama da 100 a Arewacin Najeriya Ya Rasu

  • Allah ya yi wa Basaraken Ijagbo a ƙaramar hukumar Oyun ta jihar Kwara, Oba Fagbemi, rasuwa ranar Litinin 5 ga watan Disamba, 2022
  • Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, ya miƙa sakon ta'aziyya a wata sanarwa da sakataren watsa labaransa ya fitar
  • Gwamnan ya jajanta wa iyalan Maragayin musamman Yarima da sauran 'ya'yansa kana ya yi addu'ar Allah ya masa rahama

Kwara - Wani babban Basarake, Onijagbo na Ijagbo a ƙaramar hukumar Oyun ta jihar Kwara, Oba Salawudeen Fagbemi Obembe II, ya riga mu gidan gaskiya.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa Oba Fagbemi ya kwanta dama ne ranar Litinin, 5 ga watan Disamba, 2022 yana da shekaru 110 a duniya.

Oba Salawudeen Fagbemi Obembe II.
Wani Babban Sarki Mai Shekara Sama da 100 a Arewacin Najeriya Ya Rasu Hoto: leadership
Asali: UGC

Gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya jajantawa al'ummar masarautar Ijagbo bisa rasuwar Sarkinsu, Oba Fagbemi.

Sakon ta'aziyyar mai girma gwamnan na ƙunshe ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Sakataren watsa labaransa, Rafiu Ajakaye.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wani sashin sanarwan ya ce:

"Muna miƙa sakon ta'aziyya ga majalisar Sarakunan Oyun, al'ummar Ijagba da iyalan marigayi mai martaba Sarki. Muna kuma miƙa ta'aziyya ta musamman ga Yarima Lateef Fagbemi da 'yan uwansa bisa wannan rashi."
"Marigayi Sarki ya kasance mutum mai hikima, hakuri da soyayyar mutanensa. Bawan Allah ne mai kokarin bauta masa, dukkanin mutane zasu yi matuƙar kewarsa."

Bugu da ƙari, Gwamna AbdulRazaq ya roki Allah SWT ya sa Aljannatul Furɗausy ta zama makoma ta karshe ga Marigayi sarkin.

"Muna Rokon Allah mai girma da ɗaukaka ya sa Al-jannatul Firadus ta zama makoma ga Basaraken kuma ya baiwa iyalansa da baki ɗaya al'ummar yankin Masarautarsa hakurin jure wannan gibi."

- A cewar gwamnan cikin sanarwar da Sakataren watsa labaransa ya fitar.

Ɗan takarar majalisar tarayya a Accor Party ya rasu

A wani labarin kuma Dan Takarar Majalisar Tarayya Ya Kwanta Dama Bayan Halartar Taro a mahaifarsa

Yayin da ake shirye-shiryen zuwan babban zaɓen 2023 nan da yan makonni, ɗan takarar majalisar wakilan tarayya a jihar Osun ya kwanta dama.

Rahotanni sun bayyana cewa ɗan takarar, Jacob Funmi Ogunmola, ya rasu ne bayan halartar wani taro a Saki, mazaɓar da yake neman kuri'unsu a zaɓe mak zuwa.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel