An Bude Neman Aikin Kashe Beraye A Kasar Amurka Akan Albashi 75m

An Bude Neman Aikin Kashe Beraye A Kasar Amurka Akan Albashi 75m

  • Birnin New York na neman ma'aikata na musamman da zasu taimaka wajen kawar da berayen da adadinsu ya kai miliyan 18 a birnin.
  • A cikin 2014, an kiyasta cewa kowanne dan New York na da beraye biyu,wanda hakan ke nuna akwai akalla ƙwayoyin cuta kusan miliyan 18.
  • Birnin New York na neman wanda zai yi aikin kuma ta shirye ta biya har dala $170,000 ga wanda dace.

Birnin New York na neman Jami'an da su zai taimaka wajen kawar da berayen da ke birnin wanda yawansu yakai miliyan 18. kamar yadda legit.ng ta tattaro a rahotanin da jaridun kasar Amurka suka wallafa.

A sanarwar aiki da aka buga wacce take dauke da taken Kawar da "Beraye A New York" ta nuna yadda akin yake da kuma hanyar da za'a bi wajen samun aikin.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

A cikin 2014, an kiyasta cewa akwai beraye biyu ga kowane ɗan adam a New York, yana nuna cewa yawan ƙwayoyin cuta da berayen zasu yada ko suke dauke dasu yakai kusan miliyan 18.

Beran
An Bude Neman Aikin Kashe Beraye A Kasar Amurka Akan Albashi 75m Hoto: Dkfindout
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Abubawan da ake bukata ga mai neman aiki sun hada da shedar digirin farko wanda ke nuna yayi karatu a fannin da ya shafi karatun dabbobi ko kuma yadda ake yakar cuttutukan da kwari ko dabbobi suke yadawa.

Tallan neman aikin yace:

"Beraye na taka muhimmiyar rawa wajen yada kwayoyin cuta a tsakanin al'umma, musamman ta fannin taba abubuwa da suke amfani da shi". kamar yadda tallan ya ambata .

Tallan ya ci gaba da cewa:

"ya kamata mu samu wanda zasu taya mu yakar wannan beraye tare da kawar dasu daga birnin mu sabida mu tsaftace abubuwa da suke janyo mana."

Kara karanta wannan

Ya’yan Buhari sun shiga yakin neman zaben mata na Tinubu-Shetima a Katsina

Magajin garin New York Eric Adams, ne ya rattabawa dokar daukar akin hannu tare da bada sanarwar neman aiki. Sannan Sanarwar ta kara da cewa:

"Na bayyanawa duniya karara cewa ina kyamar beraye, kuma za mu kashe su. sabida yadda suke janyo mana matsaltsalu a yankin mu."

Sashen tsaftar mahalli na gudundumar New York ta fitar da wata riga wanda farashinta yakai $48 mai dauke da taken: "Beraye suna lalata mana birni."

Yunkurin dai shine neman wanda zai aiki da kuma yadda zamu biya shi, dan kawar da da wadannan halittun

Dangote Ya Sanar Da Shirin Daukar Matasa 300,000 Aiki

A wani labarin kuma, masana’antun Dangote sun bayyana shirin daukar ‘yan Najeriya sama da 300,00 aiki a wani gagarumin shirin aikinyi da suka shirya samarwa.

An kaddamar da wani sabon shafi na daukar ma'aikatan. Idan kana tunanin ka cancanta zaka iya dora CV ɗin ka a nan.

Aikin wanda za'a bayar dashi a sabuwar matatar mai dake ta da ke Legas . Kuma wanda aka daukan zai samu faidar wurin kwana kyauta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel