Hukumar EFCC Ta Zargi Tsohuwar Minista Da Raba Kudi Dalar Amurka Miliyan 115 Dan Magudin Zaben Shekarar 2015

Hukumar EFCC Ta Zargi Tsohuwar Minista Da Raba Kudi Dalar Amurka Miliyan 115 Dan Magudin Zaben Shekarar 2015

  • Diezani ta kasance tsohuwar ministar albarkatun mai ta tarayyar Nigeria a gwamnatin GoodLuck Jonathan
  • Hukumar EFCC ta kwace kadarori da dukiya mai tarin yawa daga wajen tsohuwar ministar , kan zarginta da wawure dukiyar kasa
  • A shekarar da ta gabata EFCC ta kwato wasu kaya wanda suka hada rigar mama da dan kamfai wanda akai musu ado da zinari

Hukumar EFCC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa, Diezani Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur, ta bai wa ‘yan siyasa dala miliyan 115 domin yin magudin zaben shekarar 2015.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a ranar Laraba nan a wani taron karrama sabbin kwamishinonin zabe (INEC) da aka yi a Legas.

Bawa wanda ya samu wakilcin Adukwu Michael baban darakta a hukumar mai kula da sashen binciken laifuka, kamar yadda jaridar The cable ta rawaito

Kara karanta wannan

Badakalar N260m: Kotu Ta Yankewa Tsohon Shugaban Jami'ar Tarayya Ta Gusau shekaru 35 A Gidan Dan kande

Diezani
Hukumar EFCC Ta Zargi Tsohuwar Minista Da Raba Kudi Dalar Amurka Miliyan 115 Dan Magudin Zaben Shekarar 2015 Hoto: UCG
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mai Dezani Ta Aikata Ne

Diezani ta kasance ministar albarkatun man fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015 a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Tsohuwar ministar dai ta bar kasar nan ne kwanaki kadan kafin Jonathan ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015 .

Ana zargin tsohuwar ministar da sace dala biliyan 2.5 daga asusun gwamnatin Najeriya a lokacin da take ofis. Sai dai ta musanta zargin.

Daga shekarar 2016 zuwa yanzu EFCC tayi nasarar kwace kadarorin Diezani wanda suke hada da rukunin gidaje a Banana Island a jihar Legas.

Yayin da yake bayani game da batun tsohuwar ministan wakilin shugaban EFCC ya ce hukumar ta kwato wasu daga cikin kudaden da ake zargin Diezani ta sace.

Kara karanta wannan

Jami'iyar APC Nakasu Kawai Ta Kawo A Nigeria Tsawon Lokacin da ta Shafe Tana Mulki, Atiku

Ya bayyana cewa hukumar EFCC yaki da halayyar nan ta siyan kuri'u wanda tai kaurin suna a tsakin yan siyasa a Nigeria.

Daraktan yace:

"Hukumar EFCC ta maida hankali wajen shirya taruka da bitoci dan wayar da kan al'ummar illar siyar da kuri'a da kuma nakasun da zata kawo"
“Sau da yawa jam’iyyu siyan kuri’au masu zabe da kudi saboda ba su da ingantattun tsare-tsare da za su gamsar da masu zabe su zabe su a mulki.

Amfani Da Kudi Dan Cin Zabe

Hukumar EFCC tace ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madukwe ta biya ‘yan siyasa dala miliyan 115 domin yin Magudin zaben.

Daraktan yace:

“An kwato wasu daga cikin kudaden yayin da ake gurfanar da da yawa daga cikin masu laifin tare da yanke hukunci akan batun siyan kuri'u ko makamancin haka."
“Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC tana kara kaimi da kokarin sanya sauran masu ruwa da tsaki wajen wayar da kan al’umma kan muhimmacin kuri'arsu da kuma illar sai da ta."

Kara karanta wannan

Zargin Cin Zarafi: Uwargidan Tsohon Gwamna Ta Garzaya Gaban ‘Yan Sanda, Ta Kai Karar Wata Mata

Daga karshe ya rufe da jawabin:

“Muna aiki tare da INEC don samar da tanade-tanaden dokar zabe da kuma dokoki da suka shafi kashe kudi mai yawa a wajen yakin neman zabe ko kuma duk wata hanya ta siyan kuri'a"

Asali: Legit.ng

Online view pixel