Aisha Buhari Ce Wanda Ta Bada Umarni a Cafke Aminu Adamu Inji Kawun Matashi

Aisha Buhari Ce Wanda Ta Bada Umarni a Cafke Aminu Adamu Inji Kawun Matashi

  • An yi hira da wani baffan Aminu Adamu wanda ake zargi da cin mutuncin Aisha Buhari a Twitter
  • Kawun wannan matashi ya bayyana cewa an yi kwana da kwanaki ba a san an dauke Aminu Adamu ba
  • Ana zargin Aisha Buhari ta bada umarnin a kamo shi saboda wasu maganganu da ya yi a kan ta

Abuja - Ana kyautata zaton cewa Aminu Adamu yana tangariri a hannun jami’an tsaro na DSS a dalilin wata magana da ya yi a shafin Twitter.

Jaridar Punch ta fitar da wani rahoto a game da Aminu Adamu a ranar Litinin, 28 ga watan Nuwamba 2022, wanda yanzu ba a san inda yake ba.

Wani kawun wannan saurayi, Shehu Azare ya shaidawa Duniya cewa mahaifin yaron, Malam Adamu bai san halin da ake ciki ba, sai daga baya.

Kara karanta wannan

‘Yan Sanda Sun Yi Magana Kan ‘Kama’ Wanda Ake Zargi Ya Ci Mutuncin Aisha Buhari

Azare yace sai bayan kwanaki biyar da dauke Aminu Adamu, sannan dattijon ya samu labari.

Sai bayan kwana biyar aka ji

“Mahaifinsa bai san an cafke shi ba. Sai bayan kwanaki biyar sai wani abokin Malam Adamu ya kira shi, ya fada masa ba a ga yaronsa a makaranta ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Aka fada masa an yi kwanaki kimanin biyar ba a gan shi ba. A ranar Litinin da ta wuce kenan.
Aisha Buhari
Aisha Muhammadu Buhari Hoto: www.naijavibe.net
Asali: UGC
Sai bayan kwana daya, Aminu ya kira mahaifinsa, ya fada masa abin da yake faruwa, yace an cafke shi, Aisha Buhari ta sa an kai shi fadar shugaban kasa.

- Shehu Azare

Rahoton yace an yi wa Aminu Adamu duka bisa zargin cin mutuncin uwargidar shugaban Najeriya. Wannan mataki ya jawo Allah-wadai a Najeriya.

Kamar yadda BBC Hausa ta fitar da rahoto, daga baya jami’ar FUD da ke Dutse sun ce ba su ga dalibin ba a lokacin da ‘yan ajinsa suke zana jarrabawa ba.

Kara karanta wannan

"Don Allah Ku Yafe Wa Ɗanmu", Iyayen Aminu Azare Sun Roki Aisha Buhari Ta Yi Masa Afuwa

Kawun wannan matashi yace ya kamata yana makaranta domin rubuta jarrabawar karshe, amma kaddara ta hau kan shi, yana tsare a hannun hukuma.

Kakakin jami’ar FUD, Abdullahi Bello ya fitar da jawabi yana cewa jami’an tsaro sun bi Aminu har garin Dutse da ke Jigawa, a nan ne suka yi ram da shi.

Punch ta tuntubi Mai magana da yawun bakin uwargidar shugaban kasa, Aliyu Abdullahi domin jin ta-bakin shi, amma bai dauki kiran wayarsu ba.

Ayi hakuri

‘Yanuwan yaron mai shekaru 23 sun shiga wani mawuyacin hali a sakamakon abin da ya faru, sun yi kira ga Aisha Buhari ta taimaka, tayi masa afuwa.

A rahoton da muka fitar, an ji cewa hukumar jami'ar FUD tace ta tuntubi iyayen Aminu, sun ce suna da masaniya har sun ɗauki Lauyan da za a je kotu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel