Son Gaskiya: Wata Budurwa Ta Kai Tallafi Gidansu Suarayinta, Bidiyon Ya Ja Hankali
- Masu amfani da kafafen dada zumunta sun girgiza da ganin Bidiyon wata budurwa yar Najeriya da ta baiwa Saurayinta kyautar buhun Shinkafa
- A bidiyon mai taɓa zuciya, 'yar Najeriyan ta ja sahibinta zuwa wurin da aka aje buhun lamarin ya ba shi matuƙar mamaki
- Bayan ta barshi baki buɗe, matashin saurayin ya nemi sanin a ina sahibarsa ta samu waɗannan kuɗaɗen
Wata matashiyar budurwa ta girgiza saurayinta da iyalan gidansu da abun mamaki yayin ta gwangwaje su da kyautar Buhun Shinkafa gabanin zuwa bukukuwan Kirsimeti.
Kyakkyawan lamarin da ya faru tsakanin masoyan biyu na ƙunshe ne a wani Bidiyo da shafin jaridar @Infoxpressblog ya buga a dandalin TikTok.
A cikin Bidiyon mai ban sha'awa, budurwar ta jagoranci gishirin rayuwarta zuwa wurin da ta shirya aka aje kyautar, abinda idonsa ya gani ya jefa shi cikin farin ciki da mamaki.
Kaddara Ta Riga Fata: Kyakkyawar Budurwa Ta Kaso Aurenta Bayan Watanni 3, Ta Wallafa Hotunan Shagalin Bikin, Jama’a Sun Yi Martani
Yayin da ya tambayeta ta ya ta samu kuɗi har ta siya masa wannan kyautar, budurwar ta wayance wa tambayar tare da alƙawarin zata faɗa masa daga baya.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Nan take cikin shauki matashin ya rungume yar kyakkyawar budurwarsa yayin da yake ƙara gode mata bisa wannan karamci.
Duba Bidiyon anan
Martanin ma'abota kafafen sada zumunta
Favour yace:
"Wannan ce soyayya ta gaskiya duk yarinyar da zata iya saya mun buhun shinkafa, zan aureta."
Akpanahtammy tace:
"Ina kan kokarin samun soyayyar gaskiya saboda yaudara ta yi yawa. Ina kaunarku Allah ya barku tare."
Next Of King ya ce:
"Ina dakon sauraron budurwar da zata siya mun buhun Shinkafa a watan Disamban nan, a wata na gaba Janairu zamu yi aure."
Micky9ice1 tace:
"Addu'ata gareku Allah ya sa ku gama lafiya kuma cikin farin ciki. Nima zan zama masoyiya mai kyau amma ba mashinshini."
Gayu Gudu Na Suke Saboda Ni Kurma Ce, Tsaleliyar Budurwa Ta Koka a Bidiyo
A wani labarin kuma wata zankaɗeɗiyar budurwa ta bayyana yadda maza ke guje mata duk da kyaunta saboda wata larura da Allah ya ɗora mata
Budurwar, wacce ta bayyana abinda ke damunta da dandalin sada zumunta, tace duk saurayin da ganta yana so baya daɗewa yake kama gabansa da zaran ya gano ita kurma ce.
Sai dai mabiyansa a dandalin sun ba ta shawarar ta kwantar da hankalinta, sun faɗa mata Allah na sane da ita kuma zai bata abokin haɗin rayuwa wata rana.
Asali: Legit.ng