Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu

  • Jam'iyyar APC ta gudanar da uwar yakin neman zaben yau a jihar Legas, mahaifar dan takararta
  • Jihar Legas ta kasance karkashin mulkin jam'iyyar adawa tun daga 1999 har 2015 da Buhari ya hau mulki
  • Tinubu ya kasance tsohon gwamnan jihar har sau biyu kafin mika mulki ga hadiminsa, Fashola

Legas - Asiwaju Ahmed Bola Ahmed Tinubu, dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya lissafo jerin jihohin Arewan da ko shakka bai yi zai lashe.

Jihohin da ya lissafo sun hada da Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Kwara, da Plateau, rahoton Channelstv.

Tinubu
Jihar Kano Da Wasu Jihohin Arewa 5 Da Nike Da Tabbacin Zan Lashe: Tinubu Hoto: @OfficialABAT
Asali: UGC

Tinubu a wajen taron yakin neman zabensa da ya gudana ranar Asabar, 26 ga Nuwamba a filin Teslim Balogun dake Legas, ya yi alfaharin cewa ba ya shakka abokansa gwamnonin wadannan jihohi ba zasu bashi kunya ba.

Kara karanta wannan

Ko Shakka Babu Zan Kayar Da Peter Obi A Mahaifarsa Ta Anambra, Atiku

Yace:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

"Shin kuna ganin gwamnonin Kano, Katsina, Kaduna, Kebbi, Kwara, da Plateau? Ba zamu fadi a dukkan wadannan jihohi ba. Tare zamu mulki kasar nan. Suna nan a Legas domin nuna min goyon baya."

Tinubu ya yi kira ga al'ummar jihar Legas dake wajen taron su karbi katunan zabensu kuma su ka'da masa kuri'a a watan Febrairu.

Daga cikin wadanda ke halarce a taron akwai shugaban uwar jam'iyyar APC; Abdullahi Adamu; Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbaja; Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, dss.

Tinubu ya mulki Legas

Asiwaju Tinubu ya kasance Sanata mai wakiltar Legas ta yamma a shekarar 1992 gabanin juyin mulkin da marigayi Sani Abacha ya yi wa gwamnatin Ernest Shonekan.

Bayan mutuwar Abacha da dawowar demokradiyya, Tinubu ya lashe zaben gwamnan jihar Legas inda ya mulki jihar daga 1999 zuwa 2007.

Kara karanta wannan

Rabuwar Kan Kiristocin Arewa kan zaben 2023: Jerin wadanda suka kwancewa Babachir zani a kasuwa

Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Tinubu Ya Dira Dan takaran PDP

A jiya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya biyo ta kan Alhaji Atiku Abubakar yayinda ya tafi yakin neman zabensa masarautar Gbaramatu dake jihar Delta.

Tinubu ya shawarci Atiku tunda ya dade yana neman wannan mulki kuma har yanzu bai samu ba kawai ya hakura kuma ya janye.

Tinubu ya yiwa Atiku isgili wai shin sau nawa zai yi takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel