Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Tinubu

Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Tinubu

  • Asiwaju Bola Ahmed Tinubu na jam'iyyar APC ya caccaki abokin hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP
  • Tinubu ya yiwa Atiku isgili kan yawan takarar da yayi na kujerar shugaban kasan Najeriya
  • Tarihi ya nuna cewa tun shekarar 1992 Alhaji Atiku Abubakar ke neman kujerar shugaban kasa

Warri, jihar Delta - Dan takaran kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya caccaki abokan hamayyarsa ranar Juma'a, 25 ga Nuwamba, 2022.

Tinubu ya basu shawaran su janye daga takara saboda shi kadai ne ya cancanci zama shugaban kasa.

Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kamfen da ya je masarautar Gbaramatu dake karamar hukumar Warri dake jihar Delta, rahoton Leadership.

Su uku
Wai Sau Nawa Atiku Zai Yi Takara Ne? Ku Fada Masa Yaje Ya Huta: Tinubu
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa a 2023: Jerin Manyan Jiga-jigan APC 6 Da Basa Goyon Bayan Tinubu Saboda Tikitin Musulmi da Musulmi

Ya dira kan Atiku

Da farko, Tinubu ya yi kira da dan takaran jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, ya daina takarar kujerar shugaban kasa saboda kowace shekara sai ya nema kuma bai samu.

A cewarsa, Atiku kawai ya hakura ya janye saboda kamar yadda ya saba shan kaye, yanzu ma kasa zai sha, riwayar Channelstv.

Yace:

"Wai sau nawa Atiku zai yi takara ne? Kullun yana takara, ku fada masa yaje ya zauna, ya isa hakan."

Ya dawo kan Peter Obi

Bayana gamawa da Atiku, Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa Peter Obi kawai ya damu mutane da kididdige-kiddidigen karya da sharhin tattalin arzikin wofi.

Tinubu yace:

"Ban son ambatan sunaye, shin yana tunanin kididdige-kiddidige abinci ne yan Najeriya zasu ci? Ya bada kididdige-kiddidigen karya, lissafin banza. Ba abin da yan Najeriya ke bukata kenan ba."

Kalli bidiyon:

Tsohon Shugaban Tsagerun Neja Delta Ya Bayyana Goyon Bayansa ga Tinubu/Shettima

Kara karanta wannan

Allah Raka Taki Gona, APC Ta Maida Martani Ga Tsohon Sakataren Buhari Da Ya Zabi Goyon Bayan Atiku

A wani labarin kuwa, Asari Dokubo, shugaban Niger Delta People’s Salvation Force (NDPSF), yace yana goyon baya Bola Tinubu, ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC a zaben 2023.

A yayin zantawa da Channels TV, Dokubo ya kwatanta Tinubu, wanda tsohon gwamnan Legas ne matsayin labarin nasara a jihar.

Jaridar Daily Post ta rahoto cewa, Dokubo yace Peter Obi, ‘dan takarar shugabancin kasa na Labour Party da kuma Rabiu Musa Kwankwaso, ‘dan takarar shugabancin kasa na NNPP ba sa’o’in karawar Tinubu bane.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel