Hotunan Osinbajo da Uwargidansa Suna Murnar Cika Shekaru 33 da Aure

Hotunan Osinbajo da Uwargidansa Suna Murnar Cika Shekaru 33 da Aure

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa Dolapo Osinbajo suna murnar cika shekaru 33 da aure
  • Matar mataimakin shugaban kasan a wata wallafa da tayi a shafinta na Instagram ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba ta sanar da hakan
  • Ta wallafa wani hoto daga cikin hotunan ranar aurensu da wani kuma wanda ke bayyana sabunta rantsuwar aure da suka sake yi

Mataimakin shugaban kasan Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa Dolapow Osinbajo a ranar Juma’a, 25 ga watan Nuwamba sun cika shekaru 33 da aurensu na soyayya.

Farfesa Yemi Osinbajo da matarsa
Hotunan Osinbajo da Uwargidansa Suna Murnar Cika Shekaru 33 da Aure. Hoto daga @dolapoosinbajo
Asali: Instagram

Dolapo ta bayyana hakan a wallafar da Legit.ng ta gani a shafinta na Instagram tare da tsokacin:

“Kace “Mu tafi tare, Nace, “mu je zuwa, shekaru 33 da suka gabata.”

Dolapo, jikar mai kishin kasa da kuma wanda ya sha gwagwarmaya wurin kwatowa Najeriya ‘yancinta, Cif Obafemi Awolowo, ta auri Osinbajo a shekarar 1989.

Kara karanta wannan

Hotuna Daga Shagalin Bikin Jarumar Kannywood, Halima Atete, Jama'a Sun Yi Martani

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Auren ya samu albarkar ‘ya’ya uku masu suna Damilola, Kanyinsola da Fiyinfoluwa Osinbajo wanda ya zama ‘da daya tilo namiji.

Jama’a sun yi martani

Bayan wallafar da Dolapo Osinbajo tayi na murnar cika shekaru 33 da aure, jama’a da yawa sun taya su murna.

Ga wasu daga cikin martanin:

@moshood1655:

"Ina fatan farin ciki ya cigaba da zama har abada a gidanku, ke da iyalanki za a taya ku farin ciki da sma barka har abada. Amin. Barka da cika shekaru 33 tare da farfesa."

@adaba_emi1:

"Shekarata daya da haihuwa a wannan lokacin kuma har yanzu ban taba aure ba. Ina fatansamun irin gida kamar haka. Ina fatan samun mace tagari. Ni mawakin bishara ne."

@total_celebration:

"Ina taya ku murna da zagayowar ranar aurenku. Muna muku fatan karni masu yawa na aure mai cike da albarka."

Kara karanta wannan

Bidiyo: Matashi Ya Tashi Kan Yan Jami'a a Najeriya Bayan Ya Shiga Makaranta Da Motar Miliyan 24, Kallo Ya Koma Kansa

@seyideassistant:

"Kuma gashi nan kuna ta tafiya cikin albarka. Ina taya ku murna Farfesa Osinbajo."

Washegarin cikarsa shekaru 40, matashi ya rasu a Gombe

A wani labari na daban da Legit.ng ta rahoto, wani matashi 'dan asalin jihar Gombe ya rasu bayan kwana daya da cikarsa shekaru 40 a duniya.

Wannan na zuwa ne bayan yayi wa'zai mai ratsa jiki kan mutuwa baki dayanta

Asali: Legit.ng

Online view pixel