An Kashe Sojoji Da Wasu Jama'a Yayin Da ISWAP Ta Kai Hari a Wani Sansanin Sojoji

An Kashe Sojoji Da Wasu Jama'a Yayin Da ISWAP Ta Kai Hari a Wani Sansanin Sojoji

  • Wasu gungun 'yan ta'addan Boko Haram sun kai hari kan sansanonin sojin Najeriya a jihar Borno, sun hallaka tarin jami'an tsaro
  • Wannan lamari ya zo da muni, an hallaka wasu 'yan sanda da kuma fararen hula a wuraren da aka kai hare-haren guda biyu
  • Hukumomin tsaro sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma bayyana yadda 'yan ta'addan suka jefa bama-bamai kan wadanda basu jiba basu gani ba

Ana fargabar wasu 'yan ta'addan ISWAP sun kai farmaki sansanonin soji guda biyu a jihar Borno, sun tafka mummunar barna.

A ecwar wani rahoton da AFP ta fitar jaridar Leadership kuwa ta tattaro, 'yan ta'addan sun kai hare-haren ne a ranakun Juma'a da Asabar a wani sansanin soji da kuma gari, inda suka kashe sojoji tara.

Hakazalika, an ce sun hallaka wasu 'yan sanda biyu da kuma wani adadi na mutanen gari, kamar yadda wata majiya ta shaida.

An hallaka sojoji 9 a wani sabon harin 'yan ISWAP
An Kashe Sojoji Da Wasu Jama'a Yayin Da ISWAP Ta Kai Hari a Wani Sansanin Sojoji | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Rahoton ya kuma bayyana cewa, mambobin kungiyar ta ISWAP sun zo ne a kan motoci dauke da makamai, inda suka farmaki yankin Malam Fatori a gundumar Abadam a ranakun Juma'a da Asabar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

An saba wajen rahoto

A cewar wani rahoton SaharaReporters kuma, akalla sojoji 30 ne suka mutu a yayin wannan mummunan tari baya ga lalata kayayyakin aiki da dama na jami'an.

Kungiyar ta ISWAP ta ce, mayakanta sun mamaye wani yankin garin dauke da makamai, inda suka hallaka mutane 30 da wasu sojoji 30.

Hukumar tsaro ta tabbatar da faruwar lamarin, duk da cewa na samu bambancin rahoto daga 'yan ta'addan da kuma hukumomin tsaro.

Yadda aka ceto wadanda aka sace a wani yankin Kebbi

A wani labarin kuma, 'yan sanda sun yi nasarar ceto wasu mutanen da 'yan bindiga suka sace a wasu yankunan jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.

Labarin ya fito ne daga bakin kwamishinan 'yan sandan jihar, Ahmad Magaji Kontagora, inda ya shaidawa manema labarai yadda 'yan sandan suka yi nasarar yin aikinsu cikin tsanaki.

Hakazalika, ya bayyanawa manema labarai sunayen wadanda lamarin ya rutsa dasu, da kuma matakan da ake dauka don kakkabe ;yan ta'adda a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel