Bidiyon Kyakkyawar Matar da Ba Ta da Hannu Na Amfani da Kafafunta Wajen Yanka Kubewa Ya Ba da Mamaki
- Wata mata mai nakasa ta ba da mamaki yayin da aka ganta a wani bidiyo tana yanka kubewa da kafafunta
- A bidiyon da Diaby ta yada a kafar TikTok ranar 15 ga watan Nuwamba ta nuna lokacin da ta ke amfani da wuka wajen yanka kubewa da kafafunta
- 'Yan TikTok sun shiga mamaki, sun yi martani da irin kwarewar matar wajen aikin gida, musamman madafa
Jama'ar TikTok sun yi tururwa wajen kallon wata mata mara hannaye da ke amfani da kafafunta wajen ayyukan cikin gida.
A wani bidiyon da aka yada a kafar, an ga matar mai nakasa da ke yanka kubewa da kafafunta cikin kwarewa.
Ba a dai san me ke damun hannayenta ba, amma a bayyana yake kamar hakan bai dame ta ba, don kuwa ta yanka kubewar cikin kwarewa da kafafunta.
Ba Zan Iya Kusantar Namiji Ba: Kyakkyawar Budurwa Da Aka Nadawa Sarauta Ta Magantu, Bidiyon Ya Janyo Cece-kuce
A bidiyon mai dakiku 39, an ga tana zaune a kan kujera, ta daga kafafunta tana amfani dasu wajen yin aikin yankan kubewa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ta yi yankan da kyau, wanda da mutum zai gani zai zaci an yanka ne da hannu. Ga shi kuwa bata nuna alamar tsoron wuka za ta yanke mata kafa ba.
An kuma gano wasu sauran bidiyoyi a shafinta na TikTok, inda aka ga tana yin abubuwa daban-daban masu ban mamaki da kafafunta.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
Jama'a da dama sun yi martani a kasan bidiyon, ga kadan daga wadanda muka tattaro:
@aliyamoussa506 tace:
"Karfin hali kenan."
@Ishaq yace:
"Wow! Ina kaunarki."
@sweetneetjackson yace:
"Abin al'ajabi."
@bakisama8 yace:
"Ba zan kula da abin da mutane za su ce ba. Zan ci abin da kika dafa. Alhamdulillah. Ina ma zan iya aurenki."
Kyakkyawa Ce: Bidiyon Dirarriyar Amarya Mai Ji Da Tsawo Sanye da Takalma Masu Tsini a Ran Aurenta Ya Ja Hankali
Yaro mat talla ya ba da mamaki da kwarewarsa a lissafi
A wani labarin kuma, wani yaro mai talla ya girgiza jama'ar Instagram yayin da ya yi baje-kolin kwarewarsa a fannin lisassafi a tsakiyar.
An yada wani bidiyin lokacin da aka tsare wani yaro a hanya, aka tambaye shi ya gwada lissafa wasu lambobi, abin da ya yi ya ba kowa mamaki.
Bidiyon ya nuna yadda yaron ya amsa tambayoyin lissafi masu wahala ba tare da amfani da kalkuleta ba, hakan ya ba jama'ar Instagram mamaki.
Asali: Legit.ng